Sunday, June 7
Shadow

Tag: ilimi

Gwamnatin tarayya ta baiwa jami’o’i 12 damar fara koyarwa ta yanar Gizo

Gwamnatin tarayya ta baiwa jami’o’i 12 damar fara koyarwa ta yanar Gizo

Siyasa
Hukumar dake kula da jami'o'in Najeriya ta NUC ta baiwa jami'o'in Najeriya 12 damar fara koyar da Digiri ta yanar gizo.   An baiwa jami'o'in damar koyarda dalibai a Aji da kuma ta yanar gizo kamar yanda zamani ya kawo. Jami'o'in da aka baiwa wannan lasisi sune:   Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.   Jami'ar Abuja.   Jami'ar Maiduguri.   Jami'ar Modibo Adama.   Jami'ar Obafemi Awolowo.   Jami'ar Legas.   Jami'ar Ibadan.   Jami'ar Najeriya Nsukka.   Jami'ar kimiyya da Fasaha ta Minna.   Jami'ar jihar Legas.   Jami'ar Ladoke Akintola.   Jami'ar Joseph Ayo Babalola.
Muna fama da yunwa>>Kungiyar masu makarantu masu zaman kansu

Muna fama da yunwa>>Kungiyar masu makarantu masu zaman kansu

Siyasa
Kungiyar masu makarantu masu zaman kansu sun koka bayan da gwamnati tafe makarantun zasu ci gaba da zama a kulle har sai abinda hali yayi.   Wani jigo a kungiyar, Abdulganiyyu Raji ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace babu me tambayar halin da suke ciki. Ya kara da cewa,suna fama da yunwa da damuwa kuma tun watan Maris ba su samu sun biya ma'aikatansu Albashi ba. Yace suna bukatar gwamnati ta zo ta fara tallafa musu kamin su fara mutuwa.   Ya kara da cewa, bawai suna adawa da matakin na gwamnati bane dan suma ba zasu so saka yara da sauran masu hulda da makarantunsu cikin matsala ba amma gaskiya suna cikin wani hali.
Gwamnatin tarayya ta karyata labarin dake yawo cewa wai Ranar 8 ga watan Yuni zata bude Makarantu

Gwamnatin tarayya ta karyata labarin dake yawo cewa wai Ranar 8 ga watan Yuni zata bude Makarantu

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta karyata rade-radin dake yawo cewa wai Ranar Litinin 8 ga watan Ynmuni zata bude makarantu.   Hakan ya fitone daga bakin Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajuiba a lokacin da kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 na shugaban kasa ke bada bayani kan halin da ake ciki game da yaki da cutar a jihar. Yace ba sune suka fitar da wannan sanarwa dake yawo ba, yace ba zasu saka rayuwar Dalibau cikin hadariba.   Yace kamin su bude makarantu sai sun yi shawara da ma'aikatar Lafiya da NCDC tukuna, sun ji abinda suka ce.
Akwai tsarin bude Makarantu Kwanannan>>Gwamnatin Tarayya

Akwai tsarin bude Makarantu Kwanannan>>Gwamnatin Tarayya

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tabbas akwai shirin bude makarantu kwanannan amma ba nan da sati 2 ba kamar yanda wasu ke yadawa.   Karamin ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya bayyana haka ga manema labarai a yayin da kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 ke bayani a jiya,Juma'a. Yace suma suna so ace an koma makaranta amma ba zasi so saka rayuwar yara cikin jadari ba.   Yace akwai tsarin dawowa da makarantu kwanannan amma ba nan da sati 2 ba kamara yanda maganar ke yawo ba, yace sai sun hana da masana sun basu tabbacin cewa yaran zasu iya komawa makaranta ba tare da barazanar cutar Coronavirus/COVID-19 ba tukuna.
Gwamnatin tarayya ta bayyana guraren da za’a gina sabbin kwalejojin ilimin tarayya a jihohi 6

Gwamnatin tarayya ta bayyana guraren da za’a gina sabbin kwalejojin ilimin tarayya a jihohi 6

Uncategorized
Gwamnatin taraya ta bayyana ainahin guraren da za'a gina sabbin kwalejojin Ilimi na gwamnatin tarayya 6.   A ranar juma'ar data gabatane dai gwamnatin ta bayyana cewa zata gina sabbin kwalejojin ilimin kimiyya a bangarori 6 na kasarnan.   A sanarwar data fitar, Ma'aikatar Ilimi ta gwamnatin tarayya ta hannun daraktan kula da hukdar Jama'a, Mr Ben Goong ta bayyana cewa, ta aikewa gwamnoni takardu da sanar dasu guraren da za'a gina sabbin kwalejojin ilimin.   Yace akwai kuma wasu rade-radin karya dake yawo a shafukan sada zumunta shiyasa suka fitar da ainahin inda za'a gina Makarantun.   A Jihar Bauchi yace za'a gina makarantarne a Jama'ar, sau kuma a jihar Benue za'a ginata ne a Odugbo, Karamar Hukumar Apa, sai a jihar Ebonyi za'a ginata ne a ...
Yanzu-Yanzu:Shugaba Buhari ya amince da gina Kwalejojin Gwamnatin tarayya 6

Yanzu-Yanzu:Shugaba Buhari ya amince da gina Kwalejojin Gwamnatin tarayya 6

Uncategorized
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya amince da gina kwalejojin ilimi na gwamnatin tarayya a yankuna 6 na kasarnan.   Garuruwan da za'a gina wadannan sabbin makarantu sune; Bauchi Benue Ebonyi Osun Sakkwato Edo. Hadimin shugaban kasar,Bashir Ahmad ne ya bayyana haka ta shafinsa na sada zumunta. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1261036806277136384?s=19 A baya mun kawo muku zaman taron da shugaba Buhari yayi da shuwagabannin tsaro.
Bidiyo:Duk wanda yace an hana Sallah Azzalumine>>Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Bidiyo:Duk wanda yace an hana Sallah Azzalumine>>Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Uncategorized
Shehin Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi yayi magana akan masu cewa wannan doka ta zaman gida an hana mutane Sallah ne.   A wani faifan Bidiyo da ya watsu a shafukan sada zumunta inda aka ga yana magana yayin da yake Tafsir.   Dr. Ahmad Gumi ya jawo hankali bisa inda yace masu cewa an hana sallah Azzalumai ne.   Yace yin Sallah a gida a wannan lokaci yafi wa mutum, domin wanda yayi sallah a gida yana da lada biyu, ga ladan bin sunnar Manzon Allah (SAW) ga kuma ta yin jam'i tare da iyalai. https://twitter.com/Abdool85/status/1256963196394635265?s=19 Malam ya jawo hankalin cewa suma fa gwamnatocinnan sun fi so su bude jama'a saboda su daina ciyar dasu.   A baya dai malam yayi kira da kada a dage dokar zaman gidan.
Babu ranar da dalibai zasu koma Makaranta>>Ministan Ilimi

Babu ranar da dalibai zasu koma Makaranta>>Ministan Ilimi

Siyasa
Karamin ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba ya bayyana cewa duk da shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya sassauta dokar hana zirga-zirga da ya saka a Abuja, Legas da Ogun, babu ranar da dalibai zasu koma makaranta.   Ministan ya bayyana hakane a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai yayin ganawar da kwamitin shugaban kasa dake yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 yayi.   Yace shugaba Buhari ya bada umarnin harkar tattalin arziki ta dawo a fara kadan-kadan, sai idan abubuwa sun fara kankama sannan ne za'a san yanda za'a yi kan komawar yara makaranta.