fbpx
Friday, May 27
Shadow

Tag: Illorin

‘Yan sanda sun ceto wani da ‘yan bindiga sukai garkuwa dashi a Ilorin

‘Yan sanda sun ceto wani da ‘yan bindiga sukai garkuwa dashi a Ilorin

Crime
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kwara ta ce ta samu nasarar ceto wani mai suna Musa Atere mai shekaru 46 wanda aka sace a Ilorin da safiyar ranar Talata. Manema labarai sun ruwaito yadda masu garkuwa da mutane suka sace Mista Atere tare da nemi kudin fansa har kimanin Naira miliyan 30 daga danginsa. Sai dai A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya shaida cewa rundunar tai Nasarar ceto Mista Atere a wani kauye da ke yankin Oko Olowo a Ilorin da sanyin safiyar ranar Laraba ba tare da biyan kudin fansa ba. An dai sace mutumin ne a lokacin da suke tafiya tare da matarsa inda 'yan bindigar sukai musu kwantan bauna suka sace shi tare da kwacewa matar tasa kudaden dake wajan ta.