fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: IMF

Ba zamu yafewa Najeriya ko sisi ba sai ta biyamu kudin data ci bashi>>IMF

Ba zamu yafewa Najeriya ko sisi ba sai ta biyamu kudin data ci bashi>>IMF

Siyasa
Hukumar bada Lamuni ta Duniya, IMF ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashen da zata yafewa bashin da take bi.   Zuwa yanzu Hukumar ta ware wasu kasashe 28 da zata yafewa bashin, inda za'a yi amfani da wasu kudi da aka ajiye na ko ta kwana wajan biyawa wadanna kasashen bashin da hukumar ke binsu.   Kasashen da aka yiwa yafiyar dai sune, Afghanistan, Benin, Burkina Faso, Burundi, Central African Republic, Chad, Comoros, Democratic Republic of the Congo, Djibouti, Ethiopia, da The Gambia. Sai kuma Guinea, Guinea-Bissau, Haiti, Liberia, Madagascar, Malawi, Mali, Mozambique, Nepal, Niger, Rwanda, São Tomé and Príncipe, Sierra Leone, Solomon Islands, Tajikistan, Togo da Yemen.   Jimullar bashin da za'a yafe musu shine dala Miliyan 238.
Najeriya ta samu jimullar bashin Biliyan 11.465 daga IMF da Bankin Duniya a 2020

Najeriya ta samu jimullar bashin Biliyan 11.465 daga IMF da Bankin Duniya a 2020

Uncategorized
Hukumar bada lamuni ta Duniya, IMF da Bankin Duniya, sun baiwa Najeriya jimullar bashi Biliyan 11.465 a shekarar 2020.   Basukan an bayar dasu ne a matakai daban-daban wanda suka hada da raya yankin Arewa maso gabas, fargado da tattalin arzikin Najeriya bayan da zuwan annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ta daidaitashi, dadai sauransu. The Nation ce ta tattaro yawan bashin da Najeriyar ta ciwo a wannan shekarar ta 2020.
Matsin tattalin arzikin da Najeriya zata shiga ba zai tsannanta ba>>IMF

Matsin tattalin arzikin da Najeriya zata shiga ba zai tsannanta ba>>IMF

Siyasa
Kungiyar bada Lamuni ta Duniya, IMF ta canja hasashen da tawa Najeriya cewa zata fada matsin tattalin arziki da kaso -5.4 inda a yanzu tace kasar zata samu matsin tattalin arziki na kaso 3.4 a shekarar 2020. Hakan na nufin matsin tattalin arzikin ba zai yi tsanani kamar yanda aka yi hasashe ba.   IMF ta bayyana cewa kasashen dake fitar da danyen Mai a Duniya zasu shiga matsala saboda rashin sayen man dalilin zuwan cutar Coronavirus/COVID-19.   Gita Gopinath, IMF chief economist and director of the research department, said oil-exporting countries are battling the health and economic impact of the COVID-19 pandemic and the impact of low oil prices.   “They have been hit by the health crisis and they have been hit because they are oil exporters which h...
Zamu saka ido kan yanda za’a kashe kudin bashin da Najeriya ta ciwo daga IMF>>Majalisar Wakilai

Zamu saka ido kan yanda za’a kashe kudin bashin da Najeriya ta ciwo daga IMF>>Majalisar Wakilai

Siyasa
Majalisar wakilai ta bayyana cewa zata saka ido kan yanda gwamnatin tarayya zata kashe kudin bashin data ciwo daga hukumar bada lamini ta Duniya,IMF inda tace zata tabbatar da ganin an yi amfani da kudin yanda ya kamata.   Kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ne ya bayyana haka a yayin tattaunawar da yayi da wasu kungiyoyin dake rajin kare hakkin bil'adama.   Ya bayyana cewa akwai kuma kudirin dokar da yanzu haka majalisar dattawa ke dubawa dan mayar dashi doka wanda ya kunshi baiwa kamfanoni masu zaman kansu tallafin biyan kaso 50 cikin 100 na haraji amma da sharadin idan basu kori ma'aikata a lokacin fama da cutar Coronavirus/COVID-19 ba.   Yace kuma suna nan suna kara kokarin hada wani kufirin dokar da zai sassauta matsin da ake fama dashi a kasarnan....
IMF ta aikoma da Najeriya kudin Bashin Dala Biliyan 3.4 data bata

IMF ta aikoma da Najeriya kudin Bashin Dala Biliyan 3.4 data bata

Siyasa
Gwannatin tarayya ta bayyana cewa ta karbi kudin tallafi harna $3.4bn daga hukumar bada lamuni ta duniya, IMF. Nigeria dai ta ce zatayi amfani da tallafin da ta karba daga IMF dan farfado da tattalin arzikin kasa da cutar covid-19 gurguntar. kiristalina Geogieva,watau managan daractan ta IMF ne dai ta  bayyanawa CNBC ta Africa da cewa tuni suka turo kudin tun a ranar Laraba na $3.4bn ta asusun babban bankin nigeria, CBN. Shugaban IMF ya bukace da a yi amafani da kudin ta hanya mai kyau kuma ma a bayyana, ta yadda kuwa zai shaida. Gwamnati tarayya ta sanar cewa za ta yi kokarin yin amfani da kudin ta hanyar ciyar da Al umma, sannan kuma akwai wasu tsare tsaren da za ta fiddo dan amfanar Alumma bayan wucewar cutar. Gwamnatin dai tace zata bama IMF damar yin duk...
IMF ta amince ta baiwa Najeriya bashin Dala Biliyan 3.4

IMF ta amince ta baiwa Najeriya bashin Dala Biliyan 3.4

Siyasa
A jiya,Talata,  kungiyar bada lamuni ta Duniya, IMF ta bayyana cewa ta amince ta baiwa Najeriya bashi Dala Biliyan 3.4 data nema domin ta magance gagarumar matsalar tattalin arziki da Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ta kawowa kasar.   Saidai IMF din ta bukaci Najeriya data samar da wasu tsare-tsare na tattalin arziki da zasu farfado da tattalin arzikin kasar cikin gaggawa.   Bashin na Dala Biliyan 3.4 na cikin basukan Dala Biliyan 6.9 da Najeriya ke nema daga hukumomin dake bada bashi na Duniya dan ta magance matsalolin tattalin arziki daga kudin shiga da Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ta jefa kasar ciki.   Banda IMF, Najeriya kuma na neman bashin Biliyan 2.5 daga bankin Duniya sai kuma Bashin Biliyan 1 data ke nema daga bankin habbaka Nahiyar Af...