fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Tag: Imo

85 daga cikin masu laifi da suka tsere daga gidan yarin Imo sun Koma

85 daga cikin masu laifi da suka tsere daga gidan yarin Imo sun Koma

Uncategorized
85 daga cikin masu laifi da suka tsere daga gidan gyara hali na jihar Imo sun mayar da kansu gidan yarin.   Masu laifi 1,884 ne ake tsammanin sun tsere daga gidan gyara halin bayan harin da 'yan Bindiga wanda ake zargin 'yan IPOB ne suka kai a garin Owerri ranar Litinin.   Maharan sun lalata akalla ababen hawa 50. Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya yi alwashin yiwa masu laifin da suka koma da kansu gidan gyara halin Afuwa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta cafke wasu mutum 7 bisa laifin satar mota

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta cafke wasu mutum 7 bisa laifin satar mota

Crime
Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta dakume wasu matasa data kama da laifin satar mota kwanaki kadan bayan sakin su daga gidan gyara kan makamancin laifin. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, Orlando Ikeokwu, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya a Owerri. Ikeokwu, ya ce an samu nasarar cafke su ne bayan da rundunar ta samu rahoto daga wasu mazauna dake yankin Aba a jihar.  An dai zargi Matasan ne da satar mota kirar LEXUS 350 SUV. Sai dai lokacin da aka tuhumesu da laifin sun Amsa laifinsu.  
EFCC ta kama mutum 20 da take zargi da damfara A yanar gizo

EFCC ta kama mutum 20 da take zargi da damfara A yanar gizo

Crime
Mutum 20, da ake zargi da zamba ta yanar gizo a ranar Juma'a sun shiga hannun jami'an ofishin shiyyar na Fatakwal na Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta'anci, EFCC. Hukumar a cikin wani sako da ta wallafa a ranar Litinin ta ce an kama wadanda ake zargin ne a Owerri dake a Jihar Imo. Wadandaa aka kama sun hada da  ”Onyebuchi Victor; Isreal Victor; Emeka Clinton; Stanley Uche; Onyemachi Stanley; Ikechukwu Agbalieze; Franklin Ugoegbu; Nze Collins; Nwokoro Santus da Agocha Johnson da sauran su. Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da: wayoyin hannu guda arba'in (40), kwamfutocin tafi-da-gidanka goma sha bakwai (17) da motoci 6 tare da sauran kayyayaki. Hukumar ta ce zata gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu idan ta kammala bincike.
Wasu Fusatattu a jihar Imo sun cinnawa wasu barayi wuta da aka kama Da laifin sata

Wasu Fusatattu a jihar Imo sun cinnawa wasu barayi wuta da aka kama Da laifin sata

Uncategorized
Wasu mutane biyu da ake zargi da 'yan fashi da makami ne dubun su ta cika a loacin da aka cafke su  bayan sun yi wa wata mata fashin wayarta ta Android a garin Akuma da ke karamar Hukumar Oru ta Gabas a Jihar Imo. Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a cikin Kasuwar Afor Akuma, inda matar ta je sayen wani abu. Wasu da suka shaida mana yadda lamarin ya faru sun bayyana cewa barayin sun tare matar ne inda suka umarce ta da ta basu wayarta sai dai matar tai ta maza inda ta fallasa su wanda ya sanya jama'ar dake gurin an kara. Anyi bata kashe da 'yan fashin kafin daga bisani a cafke su yayin da mafusatan da suka dakume barayin suka cinna musu wuta sai dai wasu rahotanni sun shaida cewa a kwai daya daga cikin barayin da ya tsere. Jami'in hulda da Jama'a na rundunar 'yan s...
Jihar Imo ta samu sabon kwamishinan ‘yan sanda

Jihar Imo ta samu sabon kwamishinan ‘yan sanda

Tsaro
An Nada Nasiru Mohammed a matsayin kwamishinan 'yan sanda a jihar Imo wanda ya fara aiki a ofishin yan sanda na jihar. A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar, Orlando Ikeokwu, ya ce, sabon kwamishinan ya karbi aiki ne a ranar Alhamis daga hannun Isaac Akinmoyede, wanda aka sake sauya shi zuwa shiyya ta 17, Akure, cikin jihar Ondo, bayan karin girma zuwa mukamin Mataimakin Sufeto-Janar na’ Yan sanda (AIG) Sabon kwamishinan Muhammad dan asalin garin Zariya ne dake jihar Kaduna, yayi karatunsa a bangaran ayyukan ofis hakanan kwamishinan ya yiwa rundunar aiki a wurare daban-daban a fadin kasar.
Za’a aika ‘yansanda 3,700 wajan zaben jihar Imo

Za’a aika ‘yansanda 3,700 wajan zaben jihar Imo

Siyasa
Hukumar yansandan jihar Imo tace akalla 'yansanda 3,700 ne aka tura aiki a wajan da za'a gudanar da zabe.   Kakakin 'yansandan jihar, Isaac Akinmoyede ne ya bayyana haka a ganawa da manema labarai inda yace hukumar tasu ta shiryawa zaben sosai.   Ya bayyana cewa 'yansanda da hadin kan sauran jami'an tsaro zasu tabbatar an yi zaben cikin kwanciyar Hankali.
Ko ku shigo jam’iyyar APC ko kuma ku ci gaba da zama cikin yunwa, saidai ku yi ta Azumi>>Gwamnan Imo ya gayawa ‘yan Adawa

Ko ku shigo jam’iyyar APC ko kuma ku ci gaba da zama cikin yunwa, saidai ku yi ta Azumi>>Gwamnan Imo ya gayawa ‘yan Adawa

Siyasa
Gwamnan jihar Imo, hope Uzodinma ya bayyanawa jam'iyyun Adawa cewa ko dai su koma APC ko kuma su ci gaba da zama cikin yunwa.   Ya bayyana haka a Abuja yau, Juma'a yayin da yake magana kan komawar gwamna Dave Umahi APC da manema labarai, bayan ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.   Yace idan kana jam'iyyar Adawa saidai fa kawai kai ta Azumi. Kuma su da suke jam'iyya me mulki, sukan warware duk watsa matsala da zata taso musu cikin sauki fiye da wanda basa cikin jam'iyyar. “Once you believe in Nigeria and you have a pan-Nigeria attitude, of course, you will go for a national party. There is no gainsaying that if you are not with the national party, and you choose to be in opposition, of course, you will continue to fast until God answers your prayers. &...
Gwamnan jihar Imo yayi sabuwar dokar data bashi damar kulle duk wanda yake so har illa masha Allahu

Gwamnan jihar Imo yayi sabuwar dokar data bashi damar kulle duk wanda yake so har illa masha Allahu

Uncategorized
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya sakawa wata sabuwar doka me cike da cece-kuce hannu wadda ta bashi damar kulle duk wanda yake so har illa masha Allahu.   Dokar ta baiwa gwamnan damar sawa a kama duk wanda yake so a bisa radinsa sannan kuma ya kulleshi zuwa duk lokacin da ya ga dama. Tuni dai masana doka suka fara Allah wadai da wannan dokar da kuma neman da a soketa.
Hotuna:Gwamna Ganduje ya kaiwa Gwamnan Imo ziyara

Hotuna:Gwamna Ganduje ya kaiwa Gwamnan Imo ziyara

Siyasa
Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR tare da takwaran sa na jihar Imo Mai Girma Hope Uzodinma a gidan Tsohon Shugaban Jam'iyar APC na kasa Mai Girma Adams Oshiomole a babban birnin Benin, inda suka hadu domin ganawa ta musamman akan shirye shiryen yakin neman zaben jihar ta Edo, wanda Gwamna Ganduje ke jagorantar Kwamitin yakin neman zaben na Jam'iyar APC na kasa. Salihu Tanko Yakasai Special Adviser Media Government House Kano September 13, 2020.