
Indiya ta taya Najeriya murnar cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai
Kasar Indiya ta aike da sakon taya murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yan ci zuwa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da 'yan Najeriya gaba daya.
Hakan nakun she ne ta cikin sanarwar da Femi Adesina, ya fitar, inda ya ce sun samu wasika daga hukumomin kasar Indiya dake Najeriya wanda Shugaban kasar Indiya Ram Nath Kovind a madadin sa da mutanan kasar Indiya ke taya Najeriya murnar cikarta shekaru 60 da samun 'yancin kai.
Hakanan Shugaban ya kuma yiwa Shugaban kasa Buhari addu'ar fatan samun koshin lafiya tare da cigaba da Samun kyakykyawar dangantaka tsakanin kasashan biyu.
Najeriya Na cigaba da samun sakonin fatan Al'khairi daga sassa daban daban dake fadin Duniya domin taya ta murnar samun 'yan cin Kai.