fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tag: Indiya

Kerala wani yanki a kasar Indiya da ake musu ruwan sama mai kama da launin Jini

Kerala wani yanki a kasar Indiya da ake musu ruwan sama mai kama da launin Jini

Uncategorized
Allah Mai Iko. Tarihi ya tabbatar da cewa an samu zubar ruwan sama mai kama da launin jini a wani yanki mai suna kerala dake kasar Indiya. A wani binciken Masana da suka gudanar sun bayyana  cewa hakan na faruwa ne idan abubuwan da iska ke fitarwa ya hade da damshi damshin dake cikin gajimare. "Idan abubuwa masu launin ja dake cikin kasa suka gauraya da wannan gajimare sai launin ruwan sama mai launin jini ya samu". Tarihi ya nuna cewa an samu zubar ruwan saman mai kama da launin jini a lokuta daban-daban kamar a shekarar Alif 1896, da kuma shekarar 2001, da 2012. Bayanan da Masana kimiyya su ka yi ya zo dai dai da lamarin da ya faru a watan Juli a shekarar 2018 a kasar Rasha inda aka samu ruwan sama mai launi ja, a wani birni mai suna Norilsk.
Ana fargabar sama da mutane 100 Ambaliyar ruwa ta halaka a kasar Indiya

Ana fargabar sama da mutane 100 Ambaliyar ruwa ta halaka a kasar Indiya

Uncategorized
Rahotanni Daga Kasar Indiya. Kimanin mutane 100 zuwa 150 ne ake fargabar  ambaliyar ruwa ta yi Awon gaba dasu a can Gundumar Chamoli dake Jihar Uttarakhand ta kasar Indiya, A cewar  kamfanin dillancin labarai na ANI. Kamfanin Dillancin Labaran ya rawaito cewa tuni hukumomin kasar suka aike da kwararrun masu aikin ceto domin cetar mutane da Ambaliyar ta rutsa dasu. Ambaliyar ta haifar da karyewar babbar gadar dake a yankin tare da lallata wasu Turakun wutar lantarki wanda a halin yanzu ake kan gyarawa.  
Gobara tayi sanadin mutuwar Jariria sabbin haihuwa a kasar India

Gobara tayi sanadin mutuwar Jariria sabbin haihuwa a kasar India

Uncategorized
Wani Al'amari mai cike da ban tausayi da kuma Al'hini da ya faru a wani Asbitin gwamnati dake a yammacin Indiya inda gobara tai sanadin mutuwar wasu jariria har guda 10 al'amarin da ya sanya rudani a cikin zukatan Mazauna yankin. Lamarin Dai Ya faru a ranar Asabar a wani Asbiti dake Bhandara wanda ke a  jihar Maharashtra dake can kasar ta Indiya. A wani rahoto da aka bayyana da  cewa, a lokacin da gobarar ta tashi akwai a kalla jarirai 17 a sashin kula da masu sabbin haihuwa, yayin da 10 daga ciki aka rawaito sun mutu a sakamakon hayaki da ya turnike sashin da jaririn ke kwance, inda wasu kuma suka rasa ransu a sanadin raunin kona da suka samu yayin da ragowar Jariran 7 Ma'aikatan Asbitin suka kai ga nasarar cetowa. Sai dai biyo bayan Al'marin Tuni Dai Gwamnati ta bada Umarnin bin...
Kasar Indiya ta bayyana Shirinta na karfafa alakar tattalin arziki da Najeriya

Kasar Indiya ta bayyana Shirinta na karfafa alakar tattalin arziki da Najeriya

Kasuwanci
Indiya ta bayyana shirinta na zurfafa alakar tattalin arziki da Najeriya don bunkasa saka jari da kasuwanci tsakanin kasashen biyu. Amb Abhay Thakur, babban kwamishiann kasar shine ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da ya kaiwa Gwamna Abdullahi Ganduje a ranar Juma'a a Kano. Thakur ya bayyana cewa akwai  da dadaddiyar dangantaka da girmama juna tsakanin kasashan biyu, wanda ya samu asali tun bayan  samun ‘yancin kan  kasashen. A cewarsa, Najeriya ita ce babbar abokiyar kasuwancin kasar Indiya a Afurka. A karshe Thakur ya yi kira tare da bukatar karin  hadin gwiwar cinikayya tsakanin Najeriya da Indiya a matsayin wata hanya ta bunkasa dangantaka da huldar tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu. A nasa jawabin Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatarw...
Direban motar daukar marasa lafiya ya yi wa mai cutar COVID-19 fyade a hanyar zuwa Asbiti

Direban motar daukar marasa lafiya ya yi wa mai cutar COVID-19 fyade a hanyar zuwa Asbiti

Kiwon Lafiya
Lamarin ya farune a kasar Indiya bayan da a ka zargi wani Direban mator daukan mara lafiya Mai suna Noufal dan shekara 29 da laifin haikewa wata budurwa mai shekaru 19 wacce ke fama da cutar Coronavirus. Direban wanda a ka tura shi domin ya kai mara lafiyan zuwa cibiyar killacewa dake Pathanamthitta a daran ranar lahadi Wanda yayi dai-dai da 5 ga watan Satumba, amma gogan sai yayi amfani da damar hakan inda ya haikewa budurwar a kan hanyarsu ta zuwa Asbitin. Da isar su Asbitin ne wannan budurwa ta shaidawa jami'an Asbitin abunda ya faru da ita. Inda nan take jami'an Asbitin su ka sanar da Jami'an 'yan sanda. Daga bisani rundunar ta cafke Direban, haka zalika bayan bincike 'yan sandan sun gano Direban bashi da shaidar karatu.
Wani Dankasuwa A Kasar Indiya ya siyi Tukunkumin rufe hanci na Zinare akan kudi Dala $4’000

Wani Dankasuwa A Kasar Indiya ya siyi Tukunkumin rufe hanci na Zinare akan kudi Dala $4’000

Kasuwanci
A yayin da Duniya ke ci gaba da gwagwarmayar yaki da cutar Korona, abu daya da yazama dole shine sanya takunkumin rufe hanci domin samun kariya daga kamuwa da cutar wadda a kai imanin na da saurin yaduwa cikin al'umma. Kasancewar sanya takunkumi shine abu mafi mahimmanci da Duniya ta yadda ko ta amince da yin amfani dashi domin kaucewa yaduwar ko yada cutar coronavirus cikin jam'a. Tayu haka ne ya sanya wani Dan kasuwa Dan kasar India mai suna Shankar Kurhade wanda ke zaune a Pune dake yammacin kasar indiya, Inda ya siyi takunkumin rufe hanci na Zinare mai tsadan gaske domin samun kariya daga cutar Korona Mai saurin yaduwa. An dai bayyana cewa Dan kasuwan ya siyi takunkumin rufe hanci ne akan kimanin kudi Dalar Amurka Dala $4,000. (1.7 m) Shankar yayi Imanin cewa sanya takunkum...