
Hotuna:Anwa matasan da aka kama da laifin Zina Bulala 100 kowannensu a kasar Indonesia
Wadannan hotunan wasu matasane da aka kama a kasar Indonesia sun yi zina inda aka yanke musu hukuncin Bulala 100 kowannensu a bainar Jama'a kuma aka zartas musu da hukuncin.
Lamarin ya farune a yankin Aceh wanda ke da musulmai mafiya rinjaye. Kuma wannan yanki na zartas da hukunci bisa shari'ar Musulunci.
Sauran wanda ake wa hukunci a yankin sun hada da wanda aka kama da laifin caca da shan giya da madigo da luwadi.
Kungiyoyin dake ikirarin kare hakkin bil'adama sun sha sukar wannan hukunci da kuma kiran da a daina yinshi, shugaban kasar Indonesia shima ya kira a daina yin wannan hukunci a baya.
Mahukuntan sunce saida suka wa mutanen da za'a yankewa hukuncin bulalar gwaji dan tabbatar da lafiyarsu qalau kamin zartas musu da hukuncin. Akwai wani mutum shima...