
Zamu hana duk wanda ya aikata ba daidai ba a zaben Edo da Ondo shiga Kasarmu>>Ingila ta yi gargadi
Kasar Ingila ta yi gargadi kan zaben jihar Ondo da Edo inda tace duk wani dan siyasa da aka kama da aikata ba daidai ba to zasu hanashi shiga kasarsu sannan kuma su hanashi amfani da duk wata Kadara dake kasar.
Ingila ta kuma yi gargadin cewa, zata iya gurfanar da wanda aka samu da aikata ba daidai ba a zabukan a kotu kan dokokin kasa da kasa.
Sanarwar hakam ta fito ne daga ofishin jakadancin kasar na Najeriya ta shafinsa na Twitter. Ta bayyana jakadiyar Ingilar a Najeriya, Catriona Laing da cewa ta zauna da wakilan jam'iyyun PDP da APC inda suka tattauna kan maganar zaben.
Tace kasarsu na maraba da yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu tsakanin 'yan takarar jam'iyyun sannan tana kira da a kiyaye kada a tada hankula lokacin zabe da bayan zabe.