fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Tag: Inter Milan

Dortmund tasha kashi a hannun Freiburg yayin da Inter Milan ta lallasa Genoa

Dortmund tasha kashi a hannun Freiburg yayin da Inter Milan ta lallasa Genoa

Wasanni
Sabo dan wasan Inter Milan Eden Dzeko yayi nasarar ciwa kungiyar kwallo guda yayin data fara wannan kakar cikin nasara bayan ta lashe Serie A a kakar bara, inda ta doke Genoa daci 4-0. Yayin da ita kuwa kungiyar Freiburg ta koma ta biyu a teburin gasar Bundesliga bayan tayi nasarar lallasa Borussia Dortmund daci 2-1, inda Dortmund ta mamaye wasan amma ta kasa zira kwallaye masu yawa. Dortmund beaten by Freiburg, Inter Milan thrash Genoa Debutant striker Edin Dzeko was on target as Inter Milan got their Serie A title defence off to a flying start, thrashing Genoa 4-0 in their opening match of the season in front of fans in the San Siro on Saturday. Freiburg rose to second in the Bundesliga table on Saturday thanks to a gritty 2-1 win over a Borussia Dortmund side who dominated p...
Coppa Italia: Inter Milan suna gunadar da atisayi domin daukar fansa anjima tsakanin su da Napoli

Coppa Italia: Inter Milan suna gunadar da atisayi domin daukar fansa anjima tsakanin su da Napoli

Wasanni
Inter Milan sun cigaba da gudanar da atisayi gami da wasan na biyu na Semi final da zasu buga anjima da karfe takwas tsakanin su da Napoli, yayin da yan wasan Antonio Conte suke harin rama kwallon da Napoli suka ci su a wasan farko. A cigaba da buga wasannin kasar Italia bayan cutar korona tasa an dakatar da wasannin har na tsawon watannin hudu. Inter sun shirya rama kwallon da Fabian Ruiz ya ci su a wasan farko yayin da zasu buga wasan ba tare da yan kallo ba. Yan wasan Antonio Conte zasu yi tafiya izuwa Naples domin su kara da Napoli a wasan na biyu na Semi final, yayin da Juventus suka cancanci buga wasan karshe na gasar Coppa Italia a daren jiya saboda kwallon da suka ci wadda ba ta gida ba.
Inter Milan sun yi burus da tayin da Barcelona suka yiwa dan wasan su tare da yan wasa guda biyu

Inter Milan sun yi burus da tayin da Barcelona suka yiwa dan wasan su tare da yan wasa guda biyu

Wasanni
An samu labari daga bakin dan jarida Nicolo Schira cewa kungiyar zakarun kasar Spain sun kaddamar da euros miliyan 61 tare da Nelson Samedo da Arturo Vidal domin suyi musaya da Martinez. Kuma Barcelona sun yima dan wasan mai shekaru 22 sabon kwantirakin wanda zai ringa daukar euros 170 a kowane mako. A kafar sada zumunta ta twitter, Schira yace makonnin biyar da suka gabata Barcelona sun yiwa Martinez sabon kwantirakin da zai ringa daukar euros miliyan 10 a kowace shekara, Inter sun bukaci dala miliyan 111 akan dan wasan kuma sun yi burus da tayin da Barcelona suka yiwa dan wasan nasu na farashin dala miliyan 70 tare da Samedo da Vidal.
Bojan ya bukaci kungiyar Barcelona dasu siya tauraron Liverpool, Firmino maimakon dan Inter Milan, Martinez

Bojan ya bukaci kungiyar Barcelona dasu siya tauraron Liverpool, Firmino maimakon dan Inter Milan, Martinez

Wasanni
Barcelona suna harin siyan dan wasan Argentina Martinez wanda yaci kwallaye guda 19 a wasanni guda 32 daya buga a wannan kakar wasan kuma Kungiyar Chelsea ma suna harin siyan dan wasan. Amma tsohon dan wasan Barcelona Bojan kuma tauraron kungiyar Stoke city yace dan wasan Brazil Roberto Firmino shine yafi dacewa da kungiyar Barcelona akan Martinez. Roberto Firmino yaci kwallaye guda 77 tun da ya shiga kungiyar Liverpool a shekara ta 2015 kuma ya taimakawa kungiyar a shekarar data gabata yayin da suka lashe gasar champions lig kuma a wannan kakar wasan ma yana taka muhimmiyar rawa a kungiyar. Bojan ya gayawa Sport cewa Inter basu da wata himmar da har zata shi yaga cewa Martinez zai iya kawowa Barcelona cigaba saboda ba halayyar shi bane kuma abun kunya zai zamowa Barcelo...
Lautaro Martinez ya yarda cewa zai koma Barcelona amma inter Milan sun bukaci wani dan wasa a Barcelona

Lautaro Martinez ya yarda cewa zai koma Barcelona amma inter Milan sun bukaci wani dan wasa a Barcelona

Wasanni
Kungiyar Barcelona sun gama tattaunawa da Lautaro Martinez amma sai dai inter Milan sun bukaci Barcelona taba su dan wasan ta na tsakiya wato Arthur a cewar gwanin wasannin kwallon kafa na kasar Spain Guillem Balague. Barcelona baza su bar wannan damar ta wuce suba ta siyan Martinez amma sai dai basa so Arthur ya bar kungiyar tasu yayin da suma kungiyar Tottenham suke harin siyan dan wasan tsakiyan. Balague yace wannan ba matsala bace saboda yanzu Milan ne kadai suke harin siyan dan wasan. Barcelona suna so su siya Martinez ne domin ya maye masu gurbin Suarez saboda yana fama da raunika a wannan kakar wasan. Inter Milan sun amince zasu siyar da Martinez in har Barcelona zata basu Arthur. Balague a shafin shi na YouTube yace ba gaskiya bane Tottenham basa bukatar siyan Arthur,...