
Inyamurai sun bayyana matakin da zasu dauka idan aka hanasu shugaban kasa a 2023
Wata kungiya dake kare muradun inyamurai, Igbo National Council ta bayyana cewa tana kira ga jam'iyyun Siyasa da su tsayar sa Inyamurai a matsayin 'yan takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Sun bayar da wannan shawara ne bayan ganawar da suka yi da a Imo.
Kungiyar ta bayyana cewa idan ba'a tsayar da Inyamurai takarar shugabancin Najeriya a 2023 ba to lallai zasu nemi kafa kasar kansu.
Ta kuma yi kira ga cewa a kauracewa naman shanu dan nuna adawa ga kisan da Fulani kewa al'umma.