
Bidiyon yanda Inyamurai suka je ofishin jakadancin Kasar Ingila suna neman a kama Nnamdi Kanu
Wata kungiyar inyamurai ta Je ofishin jakandancin kasar Ingila dake Najeriya inda suka nemia kamo shugaban kungiyar IPOB, dake son kafa kasar Biafra, watau Nnamdi Kanu dan hukuntashi.
Kungiyar ta koka da cewa Kanu ya na zuga matasa suna kaiwa jami'an tsaro hari sannan kuma yana tunzurasu ana kashesu.
Yace abin takaici shine yana can kasar Ingila amma yana neman tadawa mutane hankali a Najeriya, dan hakane suke kiran a hukuntashi.
https://www.youtube.com/watch?v=cfQ6Np5M9zU
A baya hutudole.com Ya kawo muku Rahoton yanda sojoji suka kashe wasu tsagera 16 a Abia Wanda ake kyautata zaton 'yan IPOB ne