fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Iran Japan

Jakadan Japan ya bayyana Irin rawar da kasar Iran zata taka wajan samar da zaman lafiya

Jakadan Japan ya bayyana Irin rawar da kasar Iran zata taka wajan samar da zaman lafiya

Siyasa
Jakadan Iran da Japan sun tattauna kan hanyoyin fadada hadin kai da batutuwan da suka shafi Difulomasiyar kasashan biyu a garin Moscow dake kasar Rasha. Kazem Jalali da Toyohisa Kozuki sun tattauna batutuwan da suka shafi yankunan , gami da hadin gwiwar siyasa da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Jalali ya jaddada rashin bin doka da matakin da kasar Amurka ke dauka kan Iran da kokarin maido da takunkumin, duk da adawar da duniya ke nunawa, musamman mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. Ya kara da cewa an hana Iran bukatun tattalin arziki da siyasa na JCPOA saboda zagon kasar Amurka. Jakadan na Japan ya jaddada rawar da Iran za ta taka wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. News Islam Agency.