
An rataye wani zakaran wasan kokawa a Iran
Hukumomi a ƙasar Iran sun zartar da hukuncin kisa kan wani zakaran wasan kokawa mai suna Navid Afkari duk da kiraye-kirayen da aka yi na yi masa afuwa.
An rataye Afkari ne a wani gidan yari da ke birnin Shiraz. An zarge shi da kashe wani jami'in tsaron gidan yari yayin wata zanga-zangar ƙin jinin gwamnati shakara biyu da suka wuce.
Shari'ar Afkari ta ja hankalin ƙasashen duniya, wanda ya ce an azabtar da shi har sai da ya masa laifin aikata kisan.
Shugaban Amurka Donald Trump ya roƙi Iran da ta yi masa afuwa, yayin da su ma hukumomin wasanni na duniya suka saka baki.
BBChausa.