
Yanzu-Yanzu gwamnati ta bayar da umurni a dakatar da dukkan wani layin waya da ba’a hada shi da NIMC ba
Ministan sadarwa Aliyu Isa Fantami ya bayyana a safiyar ranar litinin cewa gwamnati ta bayar da umurni a dakatar da dukkan wani layi daga kiran waya idan har ba'a hada shi da NIMC ba.
Inda ya kara da cewa wannan dokar zata fara aiki ne daga yau 4/4/2022. An saka wannan dokar ne domin a magance matsalar tsaro a kasar.
Yayin da gwamnati ta fara bukatar mutane su hada layikansu da NIMC din tun a watan disemba na shekarar 2020.