
Yanzu-Yanzu:Gwamnatin Kano ta rufe makarantun Islamiya saboda Coronavirus/COVID-19
Gwamnatin jihar Kano ta dauki matakin rufe makarantu Islamiya dan kaucewa yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.
Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya tabbatar da haka ta shafinsa na sada zumuntar Twitter.
https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1241752193826533377?s=19
Matakin na zuwane bayan gwamnatocin jihohin Najeriya suka kulle makarantu da hana taruwar jama'a.