
Tarzoma ta barke tsakanin ‘yan Boko Haram suna ta kashe junansu
Mayaƙan ISWAP da na Boko Haram ɓangaren Abubakar Shekau sun yi mummunan artabu da juna kan iko da wani yanki a Tafkin Chadi.
Jaridar PRNigeria ta ce ƴan ta’adda aƙalla 54 aka kashe cikin wata ɗaya a artabu tsakanin mayaƙan ISWAP da na Boko Haram ƴan ƙabilar Buduma a Jamhuriyyar Nijar.
A cewar jaridar ƴan Boko Haram daga ƙabilar Buduma suka fara kai wa ISWAP harin ba-zata a ƙauyen Chikka da ISWAP ke iko da shi a ranar 3 ga watan Maris domin kwasar ganima.
“Mayaƙan daga ɓangaren Shekau sun mamaye ƙauyen inda suka kashe ƴan ISWAP da dama tare da sace matansu guda biyar. Kuma mayaƙan sun saci kayayyakin abinci kafin su gudu a cikin dare.”
Daga baya kuma ISWAP ta kai harin ramuwar gayya inda suka yi ɓarin wuta da ƴan Boko Haram a yankin Kaduna Ruwa da Kaiga kuma an yi hasarar rayuka...