fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Italiya

Yan kasar Italiya na zanga-zanga basu so a sake saka musu dokar kulle saboda Coronavirus/COVID-19

Yan kasar Italiya na zanga-zanga basu so a sake saka musu dokar kulle saboda Coronavirus/COVID-19

Siyasa
'Yan kasar Italiya na zanga-zanga a Birnin Rome na kasar aboda adawa da saka musu dokar kulle dalilin dawowar Coronavirus/COVID-19.   Saidai zanga-zangar ta koma rikici inda masu zanga-zangar suka rika wurgawa 'yansanda Kwalabe da sauran abubuwa.   Kamfanin dillancin labaran Ansa News ya ruwaito cewa zanga-zangar ta watsu zuwa wasu garuruwan na kasar inda wasu ke neman gwamnati ta basu tallafi saboda matsalar tattalin arzikin da cutar Coronavirus/COVID-19 ta saka su.   Protests against the Italian government’s coronavirus policies turned violent on Saturday, with clashes breaking out between police and demonstrators in the nation’s capital, Rome.   According to media reports, several hundred people gathered in central Campo de’ Fiori to protest a...
Coronavirus: Sai a watan Satumba zamu bude makarantunmu>>Kasar Italiya

Coronavirus: Sai a watan Satumba zamu bude makarantunmu>>Kasar Italiya

Kiwon Lafiya
Kasar Italiya wadda na daya daga cikin kasashen dake gaba-gana da cutar Coronavirus/COVID-19 ta fi yiwa Illa a Duniya ta bayyana cewa sai nan da watan Satumba zata bude makarantunta.   Mutane akalla Dubu 26 ne suka Mutu asanadin cutar a kasar wanda hakan ke nufin itace kasa ta 2 a Duniya da cutar tafi yin kisa bayan kasar Amurka.   A jiya,Lahadi mutane 260 ne suka rasu sanadin cutar a kasa wanda rabon da mutane kalilan haka su mutu sandin cutar tun Ranar 14 da watan Maris da ya gaba.   Sannan hakan ci gaba ne idan aka kwatanta da mutane 415 da suka mutu a Ranar Asabar din data gabata a kasar.   Firai ministan kasar, Giuseppe Conte ya bayyana cewa nan da Ranar Litinin, 4 ga watan Afrilu zasu bude masana'antunsu su fara aiki.   Saida...
Kasar Italiya na ganin tashin hankali: Coronavirus/Covid-19 ta kashe mutane 627 a kwana daya

Kasar Italiya na ganin tashin hankali: Coronavirus/Covid-19 ta kashe mutane 627 a kwana daya

Kiwon Lafiya
Hukumomin Kasar Italiya sun ce, yau juma’a mutane 627 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus ko kuma COVID-19 abin da ya kawo adadin mutanen da suka mutu a kasar zuwa 4,032.   Alkaluman mutanen da suka kamu da cutar a Italiya sun zarce 47,000 sakamakon karuwar mutane kusan 6,000 a cikin sa’oi 24.   Kasar da ke dauke da mutane miliyan 60 yanzu ita ce kan gaba cikin jerin kasashen da wannan annuba tafi yi wa illa, yayin da China da ta samu nasarar dakile cutar  ta koma ta biyu.   Matteo Bassetti, daraktan da ke kula da Ma’aikatar Yaki da Cutuka Masu Yaduwa ya ce, yanzu haka akwai mutane da dama da ke dauke da cutar kuma suna yada ta.   Gwamnatin Italiya na nazarin daukar matakin kara wa’adin zaman gida da rufe wuraren sana’oi fiye da ranar...
Kasar Italiya ta killace mutane sama da Miliyan 15 saboda Coronavirus

Kasar Italiya ta killace mutane sama da Miliyan 15 saboda Coronavirus

Kiwon Lafiya
Gwamnatin Italiya ta dauki matakin killace kashi 1 bisa 4 na daukacin al’ummar kasar, bayanda a safiyar yau ta dakatar da shige da fice a yankin arewacin kasar, don dakile yaduwar annobar murar Coronavirus dake barna a kasar.   Matakin killace arewacin kasar ta Italiya da ya shafi sama da mutane miliyan 15, zai ci gaba da wanzuwa har ranar 3 ga watan Afrilun dake tafe, inda dole sai da kwakkwaran dalili za a baiwa mutane damar shiga yankin arewacin Italiyan, ciki har da biranen Venice da Milan.   A wani matakin kuma gwamnatin Italiyan ta rufe baki dayan gidajen Sinima, filayen wasannin kalankuwa da kuma gidajen adana kayan tarihi dake kasar, duk dai kan annobar murar ta Coronavirus.   Jami’an lafiya sun ce yanzu haka annobar ta Coronavirus ta halaka mutane ...
Ronaldo ya buga wasa na Dubu 1 a Rayuwarsa: Kadarin cin kwallonsa ya karye: Karanta sauran abubuwan kayatarwa na wasan da Juve ta ci Inter 2-0

Ronaldo ya buga wasa na Dubu 1 a Rayuwarsa: Kadarin cin kwallonsa ya karye: Karanta sauran abubuwan kayatarwa na wasan da Juve ta ci Inter 2-0

Wasanni
Tauraron dan kwallon kafa na kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo ya buga wasanni 1000 a rayuwarsa.   Hakan ya tabbatane bayan wasan daya bugawa Juve da ta kara da Inter Milan a daren Ranar Lahadi,wasan da ya kare da sakamakon 2-0 bayan kwallayen Aaron  Ramsey da Dybala suka ciwa kungiyar.   Wani abin kayatarwa da wannan mataki da Ronaldo ya kai shine, wasanshi na farko a kungiyarshi ta Sporting da Inter Milan suka kara.   Wannan nasarar na nufin Juventus ta hau saman teburin Serie A da maki 63, inda ta baiwa Ta Kasanta, Lazio tazarar kaki 1, sai Kuma Inter Milan dake ta 3.   An tashi wasan Ronaldo be ci kwallo ko da guda daya ba wanda hakan ke nufin cewa kadarin Ronaldon na jera wasanni 11 yana cin kwallo a kowanne ya karye.   Wani ab...