
Rashin Tsaro: Shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin sake bude iyakokin Nageriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Talata, ya gaya wa gwamnoni 36 cewa Gwamnatin Tarayya na shirin sake bude kan iyakokin kasar nan bada jimawa ba.
Shugaba Buhari, wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi da gwamnonin jihohin kan batun tsaro, ya bukace su da su kara yin aiki tare da sarakunan gargajiya da membobin al'umma don inganta tattara bayanan cikin gida wanda zai taimaka wa ayyukan hukumomin tsaro.