fbpx
Friday, May 27
Shadow

Tag: Izala

Kungiyar Izala ta yi Allah wadai da halayyar shugaban Faransa

Kungiyar Izala ta yi Allah wadai da halayyar shugaban Faransa

Siyasa
Shugaban Kungiyar Izala a Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi Allah-wadai da shugaban Faransa Emmanuel Macron, saboda goyon bayan zanen batanci ga Annabi Muhammad. Da yake jawabi a wani bidiyo da shafin kungiyar na Najeriya ya wallafa a Facebook, shugaban ya ce ba dai-dai bane ƴancin faɗin albarkacin baki ya zama hanyar ɓata addini ko abin da wasu suka yi imani da shi. ''Babu shakka ya kamata shugabanFaransa da sauran ire-irensa su gane cewa addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, don haka ko kowanene a duniya ya soki Annabi, dole ne musulmai daga ko ina su kare addininsu'' A cewar malamin Annabi ya zauna da wadanda ba musulmai ba a Madina, amma akwai gurin da basa yarda su taba.
Duk Wanda Ya Fadi Sharri A Kanmu, Ku Fadi Alkairi A Kansa>>Sheik Bala Lau

Duk Wanda Ya Fadi Sharri A Kanmu, Ku Fadi Alkairi A Kansa>>Sheik Bala Lau

Uncategorized
Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya yi kira ga marubuta musamman na dandalin 'FACEBOOK' dake tafka muhawara akan gayyatar da aka aikewa Sheikh Jingir zuwa wajen aza tubalin gina jami'ar AS'SALAM' mallakar kungiyar IZALA. Sheikh Bala Lau ya ce babu dalili da za a yi hakan a musulunci, laifi ne babba a dinga cin mutuncin juna.   Shugaban ya kara da cewa, nasara muke nema a wajen Allah, kuma mun samu, to me zai sa ka biyewa wani wanda bai fahimci hakan ba, inaga yakamata mu maida hankali akan abun da ya shafe mu, maimakon nemawa kawuna zunubi.   ''Daga yanzu Ina umurtan wadanda ke rubutu da sunan masu kare mu cewa, kada kowa ya sake irin wannan rubutu ga kowaye, ku mutunta kowane Malami. Idan wani ya fadi sharri akan mu, to ku, ku fadi alheri akansu,...
Rashin Ilimin Addini Ne Ke Haifar Da ‘Yan Ta’adda>>Sheikh Bala Lau

Rashin Ilimin Addini Ne Ke Haifar Da ‘Yan Ta’adda>>Sheikh Bala Lau

Uncategorized
An bayyana cewar rashin samun ilimin addinin Musulunci yadda ya kamata shine ke haifar da samuwar 'yan ta'adda musamman a yankin Arewacin Najeriya. Shugaban kungiyar Izala na ƙasa baki daya Imam Abdullahi Bala Lau ya bayyana hakan lokacin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.   Sheikh Lau ya ƙara da cewar a halin yanzu Ƙungiyar ta su za ta mayar da hankali sosai wajen yin da'awa da karantar da Fulanin Daji da ke rayuwa a rugage, kasancewar yadda ake yawaitar samun 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane a cikin su a wannan zamani.   "Haƙiƙa ilimin addinin Musulunci shine ke gyara rayuwar al'umma, ya mayar da su bisa tsari, muna da yakinin muddin muka juya ga bangaren ilimantar da Fulani Makiyaya addini, babu shakka za'a samu nasara wajen daƙile yaɗuwa...
Shugabannin Kungiyar Izala Sun Kaiwa Bafarawa Ziyarar Godiya Kan Kyautar Makekiyar Makarantar Da Ya Ba Su

Shugabannin Kungiyar Izala Sun Kaiwa Bafarawa Ziyarar Godiya Kan Kyautar Makekiyar Makarantar Da Ya Ba Su

Siyasa
Majlisar koli ta kungiyar JIBWIS, tare da wasu wakilan kwamitoci a matakin kasa da wasu takaitattun shugabannin jihohi sun ziyarci Tsohon gwamnan jihar Sokoto Dakta Attahiru Dalhatu Bafarawa, domin yi masa godiya akan kyautar makekiyar makaranta wanda ya kashe mata sama da miliyan dubu daya da dari biyar a shinkafin Jihar Zamfara. Shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau shi ya jagoranci tawagar tare da manyan malaman kungiyar. "Mun niko gari takanas ta kano domin muzo da dukkan mutanen mu dake fadin Naijeriya, mu nuna farin cikin mu na kyautar wannan makaranta da ka yiwa wannan kungiya mai albarka, kuma bamu da wani Abu da zamu maka illa muyi ta maka addu'a Allah ya saka maka da gidan aljanna" inji Sheikh Bala Lau. A lokacin da yake mai da bayani, Tsohon gwamna Attahiru Baf...
Kungiyoyin Agaji Na Shi’a, Izala Da Darika Sun Yi Aikin Gyaran Asibiti Tare A Garin Bakori

Kungiyoyin Agaji Na Shi’a, Izala Da Darika Sun Yi Aikin Gyaran Asibiti Tare A Garin Bakori

Siyasa
A ranar Lahadi 28/06/2020 wasu gamayyar kungoyoyin bada agaji da taimako da suka hada da Harisawa daga bangaren Shi'a da Kungiyar bada Agaji ta Izala da kuma 'Darika suka hadu waje guda inda suka gudanar da gagarumin aikin gayya domin tsaftace da gyara babban Asibiti garin Bakori dake Jihar Katsina gami da temaka marassa lafiya da abubuwa da dama. Yayin aikin an share dukkan haraban asibitin sannan aka hada da ciki wajan kwantar da masu jinya. An wanke dukkan ciki da waje da amfani da sabulun kashe cutuka, an gyara wasu abubuwan da suka lalace. An cire dukkan datti hatta a makwantan masu jinya. An hada hatta bayikan zagawa sannan aka yi feshin maganin cutuka da kuma kwari, daga karshe aka dauki hotuna aka watse. Rariya.
Hotuna: Shugabannin Izala Sun Halarci Daurin Auren ‘Dan Marigayi Sheikh Ja’afar

Hotuna: Shugabannin Izala Sun Halarci Daurin Auren ‘Dan Marigayi Sheikh Ja’afar

Uncategorized
A safiyar yau Asabar ne Shugaban kungiyar Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya halarci daurin auren dan gidan marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, wato Ustaz Saalim Ja'afar Mahmud Adam.   Sheikh Dr. Bashir Umar Ali, shine wanda ya karbi auren, Sheikh Bala Lau shi kuma ya daura auren, inda Sheikh (Dr) Muhammad Kabir Haruna Gombe ya gabatar da addu'oi. Allah ya sanya albarka a wannan aure. Allah Yaji kan Malam Jafar Mahamud Adam Kano Daga Umar Gaya
Kungiyar Izala Ta Yi Allah Wadai Da Kashe-kashen Da ‘yan Ta’adda Ke Yi A Yankin Arewa

Kungiyar Izala Ta Yi Allah Wadai Da Kashe-kashen Da ‘yan Ta’adda Ke Yi A Yankin Arewa

Uncategorized
Kungiyar wa'azin musulunci ta JIBWIS ta nuna alhininta da matukar damuwa akan kashe-kashen bayin Allah da basuji ba, basu gani ba da ake yi a Jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Borno da sauran su. Hakan ya fito ne daga bakin Shugaban JIBWIS Sheik (Dr) Abdullahi Bala Lau a wani zantawa da yayi da 'yan jaridu a maraicen Asabar din jiya.     Shehin Malamin ya nuna damuwarsa matuka akan kisan kiyashi da ake yi a yankin arewa maso gabar, da arewa maso yamma, ''Ina mika sako na musanman ga Gwammatin tarayya cewa wannan kashe-kashen da ake yi fa yayi yawa, koda rai guda ne wajibine Gwannati ta kare ballantana rayukan mutane masu yawa. Dole Gwamnati ta sake nazari domin tsare rayukan Jama'arta, tun mutane basu fara daukan makami domin kare kansu ba, wanda a karshe ana iya samun w...
Rikicin limanci tsakanin izala da darika ya jikkata mutum takwas

Rikicin limanci tsakanin izala da darika ya jikkata mutum takwas

Uncategorized
Rikicin limanci a babban masalacin juma’a na garin Okene a tsakanin ‘ya’yan kungiyar Izalatul bidi’a wa’ikamatus sunnah da na ‘yan darikar Tijjaniya ya jikkata mutum takwas a jihar Kogi.     Majiyar Aminiya ta shaida cewa tun bayan rasuwar babban limamin masalacin, Shaikh Musa Galadima a shakarar 2019,  ake samun tashin tashana a tsakanin kungiyoyin biyu akan wanda zai gaji marigayin,  ya ci gaba da bada sallah a matsayin sa na babban limami a masallacin.     Wasu da suka shaida faruwar Lamarin sun shaida wa Aminiya cewa, rikicin da ya faru a ranar juma’a, 15 ga watan Mayu ba shi ne irin sa na farko ba a masallacin domin a baya ma an taba kwata irin  hakan a tsakanin kugiyoyin Islama biyu masu banbancin ra’ayi inda ko wane bangare ke fatan jan raga...
An Yi Ca Akan Jaridar Sahara Reporters saboda buga Labarin mutuwar shugaban Izala, Bala Lau

An Yi Ca Akan Jaridar Sahara Reporters saboda buga Labarin mutuwar shugaban Izala, Bala Lau

Uncategorized
Jaridar Sahara Reporters ta yanar gizo na fuskantar kakkausan suka a shafukan sada zumunta musamman ma a Twitter bayan da ta wallafa wani labari da ke cewa shugaban kungiyar izala a Najeriya Sheikh Bala Lau ya rasu.   Sai dai shugaban ya fito ya musanta lamarin a cikin wani faifan bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta.   “Mai kokarin cewa zai wallafa labarin mutuwar wani, idan ya yi hakuri sai ta Allah ta kasance a kan sa.”   “Ni lafiya ta kalau kuma ban san me ya sa suka rubuta wannan labarin ba.”   Wannan al’amari na faruwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta Izala ta yi rashin babban malaminta Sheikh Adamu Gashua a jihar Yobe.     A lokacin da Sahara Reporters ta fitar da sanarwar cewa shugaban ya rasu, sun k...