
Jadon Sancho ya shirya komawa kungiyar Manchester United>>shugaban Dortmund
Tauraron dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Dortmund, Jadon Sancho yayi nasarar cin kwallon shi ta farko a wannan kakar bayan Akanji ya fara zira kwallo a wasan su da Wolfsburg wanda hakan yasa Dortmund ta koma ta hudu a saman teburin gasar Bundlesliga.
Jadon Sancho ya kasance babban dan wasan da kungiyar Manchester tayi kokarin siya a kakar bara, amma sai dai ta kasa biyan farashin da kungiyar Dortmund ta sawa tauraron dan wasan nata.
Amma yanzu an samu labari daga gwanin kasuwar kwallon kafa, Fabrozio Romano na cewa shugaban kungiyar Dortmund Watzke ya bayyana Jadon Sancho ya shirya komawa kungiyar Manchester United.
Romano ya kara da cewa dan wasan ba zai bar Dortmund a wannan kasuwar ta watan janairu ba, amma a karshen wannan kakar ne kungiyoyin tamola zasu fafata wurin siyan ...