fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Jahar kano

Jihar Kano ta sake sallamar karin mutum 43 da suka warke daga cutar coronavirus/covid-19

Jihar Kano ta sake sallamar karin mutum 43 da suka warke daga cutar coronavirus/covid-19

Kiwon Lafiya
Ma'aikatar lafiya ta jihar kano ta sake fidda sanarwar sallamar karin mutum da suka warke daga cuta mai sarke Numfashi wato Coronavirus.   Sanarwar ta fito ne ta shafin hukumar  dake kafar sada zumunta inda hukumar ta bayyana cewa an sake samun karin mutum 16 da cutar ta sake kamawa. https://twitter.com/KNSMOH/status/1361786723131412485?s=20   Kano.
Gwamnatin Kano ta rufe wasu haramtattun shagunan magunguna

Gwamnatin Kano ta rufe wasu haramtattun shagunan magunguna

Kiwon Lafiya
Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wasu shagunan sayar da Magunguna sakamakon kin cika wasu ka'idoji na hukuma da suka hada da rashin yin Rijistar. Babban sakataren hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu na jihar Kano (PHIMA), Dakta Usman Tijjani Aliyu a ranar Laraba ne ya sanar da rufe shagunan inda ya ce jihar ba za ta amince da yanayin da wasu mutane za su jefa lafiyar mazauna jihar cikin matsala ba saboda bukatunsu na kashin kai. Dakta Usman Tijjani Aliyu ya ce an gudanar da atisayen ne tare da hadin gwiwar kungiyar hada magunguna ta kasa (PCN) a unguwar Darmanawa dake karamar hukumar Tarauni a jihar kano Ya ce za a ci gaba da binciken wuraren da abin ya shafa tare da daukar matakan da suka dace daidai da dokokin PCN.
Hotuna: Jam’iyyar PDP reshan jihar Kano ta samu sabbin shuwagabannin jihar

Hotuna: Jam’iyyar PDP reshan jihar Kano ta samu sabbin shuwagabannin jihar

Siyasa
Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano a ranar Litinin ta zabi sabbin shugabannin gudanarwa da za su tafiyar da al’amuran jam’iyyar na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Wasu daga cikin zababbun shuwagabannin sun hada da Shehu Wada Sagagi a matsayin sabon shugaban jiha, Dankaka Hussaini Bebeji (Mataimakin Shugaba), Jamilu Abubakar Dambatta (Sakatare), Idris Zarewa (Ma'aji), Halima Uba Jalli (Shugabar Mata), Hafizu Sharif Gambo (Shugaban Matasa), Sunusi Sirajo Kwankwaso (Sakataren Shiryawa), Bashir Aminu Sanata (PRO) Dahiru Maitama Abdullahi (Sakataren Kudi) da Auwalu Nagero (Odita) da sauransu.    
Hatsarin mota yayi sanadin rasa rayukan mutane 8 a jihar Kano

Hatsarin mota yayi sanadin rasa rayukan mutane 8 a jihar Kano

Uncategorized
Wani Mummunan hadarin mota da ya faru akan titin Wudil zuwa bauchi ya yi sanadin salwantar rayukan mutane 8 tare da jikkata wasu mutum 6. Lamarin dai ya faru ne a ranar Al'hamis a lokacin da wata mota kirar Volkswagen Sharan, dauke da fasinjoji tai taho mugama da wata motar a dai dai kauyan Dakare da ke karamar hukumar Garko a jihar kano. Jami'in hukumar kiyaye hadura na jihar Kano Zubairu Mato, shine ya tabbatar da faruwar lamarin a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya NAN a jihar Kano. Ya bayyana cewa, sun samu kiran wayane daga yankin kan lamarin da misalin karfe 9 dai-dai na safe, inda daga jin haka hukumar ta aike da jami'anta domin ceto wandanda lamarin ya rutsa dasu. Da yake karin haske kan lamarin jami'in hukumar kiyaye haduran ya shaida cew...
Ma’aikatar Noma ta kasa ta bayyana cewa Manoma 500,000 ta yiwa rajista a jihar Kano

Ma’aikatar Noma ta kasa ta bayyana cewa Manoma 500,000 ta yiwa rajista a jihar Kano

Uncategorized
Ma’aikatar noma da bunkasa karkara ta yiwa manoma sama da dubu dari biyar rijista a jihar Kano. An ruwaito cewa Ministan Noma Sabo Nanono, shine  ya bayyana hakan, a ranar Litinin, a lokacin da yake kaddamar da atisayen hana yaduwar kwari na kasa a filin jirgin saman Malam Aminu Kano dake jihar kano. Ministan ya ce kawo yanzu ma’aikatar ta yi wa manoma sama da miliyan biyar rajista a kasar. A cewarsa, Gwamnatin Shugaba Buhari ta himmatu wajan bunkasa harkokin noma a fadin kasar domin dakile tasirin da cutar Covid-19 ta haifar ga tattalin arzikin kasa. Sai dai ya yaba da gagarumar gudummawar da gwamnatin jihar Kano ke bayarwa wajen bunkasa harkar noma, inda ya kara da cewa tare da hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki za a iya kawar da duk wasu matsaloli da za su haifar da farga...
Gwamnatin jihar Kano ta nemi hukumar NDLEA da ta gudanar da gwajin kwayoyi ga ‘yan takarar zaben kananan hukumomin jihar

Gwamnatin jihar Kano ta nemi hukumar NDLEA da ta gudanar da gwajin kwayoyi ga ‘yan takarar zaben kananan hukumomin jihar

Siyasa
Gwamnatin jihar Kano ta nemi hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da ta gudanar da gwajin kwayoyi ga dukkan ‘yan takarar jam’iyyar  (APC) a zaben kananan hukumomin jihar da su ka hada da   shuwagabanin karamar hukumar da kansiloli. Wannan na kunshe ne ta cikin wata wasika da ta fito daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji wanda ya samu sa hannun daga Sakatariya ta din-din kan sha'anin al'amuran siyasa Hajiya Bilkisu Shehu Mai Mota. Sanarwar wacce Sakataren yada labarai Uba Abdullahi ya baiwa manema labarai ta ce gwajin ya kasance wani bangare ne na kokarin tabbatar da kyakkyawan aiki da taka tsantsan da bin diddigin dabi'un zababbun shuwagabannin da  za a baiwa jagorancin Jama'a.    
Gwamnatin Kano Ta Shirya Gina rukunin Gidaje A Masarautu 5 Na Jihar

Gwamnatin Kano Ta Shirya Gina rukunin Gidaje A Masarautu 5 Na Jihar

Siyasa
Gwamnatin Jihar Kano ta ce an gabatar da Naira miliyan 30 a cikin kasafin kudi na 2021 don fara aikin gina rukunin gidaje a fadin Masarautu biyar da ke jihar, a cewar Kwamishinan Gidaje da Sufuri na Jihar, Alhaji Mahmud Muhammad. Kwamishinan  wanda ya shaida haka jim kadan bayan ya bayyana a gaban kwamitin majalisar jihar, kan harkokin Sufuri da Gidaje a ranar Litinin, domin kare alkaluman kasafin kudin na shekarar 2021, ya bayyana kananan hukumomin Masarautar da za su ci gajiyar aikin wadanda su ka hada da Kano, Rano, Gaya, Karaye da Bichi. Ya ce an tsara adadin kudin ne don saye da kuma fidda fili a fadin Masarautun, inda za a tsara filayen. Hakazalika, Manajan Daraktan, Hukumar Kula da Hanyoyi ta jihar Kano (KAROTA), Alhaji Baffa Dan'agundi ya ce hukumar tana gudanar da ayyukan...
Gwamnatin tarayya zata gina hanyoyin mota masu nisan kilomita 65 domin bunkasa harkar noma a jihar Kano

Gwamnatin tarayya zata gina hanyoyin mota masu nisan kilomita 65 domin bunkasa harkar noma a jihar Kano

Uncategorized
Gwamnatin Tarayya ta fara aikin gina hanyoyin mota masu nisan kilomita 65 a kananan hukumomin kibiya, karaye, Rano da bunkure dake jihar Kano, don karfafa noman. Alhaji Kabir Alhassan-Rurum Dan Majalisar tarayya Mai wakiltar - Rano / Kibiya / Bunkure shine ya bayyana hakan, a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba a Kano. Ayyukan, in ji shi, an tsara su ne don saukaka zirga-zirgar kayan gona da kuma hada manoman jihar Kano da takwarorinsu na jihohin Kaduna, Jigawa da Bauchi. Alhassan-Rurum ya kara da cewa gwamnati ta kammala shirye-shiryen rarraba injinan bar ruwa da sauran kayan aiki ga manoman yankin. Hakanan Dan majalisar ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa Asbitin Gwamnatin da kuma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya a m...
Iyayan da a ke zargi da daure Dansu tsawan shekara 7 sun gurfana a gaban Kotu a jihar Kano

Iyayan da a ke zargi da daure Dansu tsawan shekara 7 sun gurfana a gaban Kotu a jihar Kano

Uncategorized
An gurfanar da Mahaifan da suk Daga jihar Kano. Mahaifin Ahmad Aliyu (Namama) tare da kishiyar babarsa sun gurfana a gaban kotun majestire dake da zamanta a Zungeru a yankin sabon gari dake jihar kano, bisa tuhumar su da laifin hada baki tare da Daure dansu mai suna Ahmad Aliyu Namama har tsawan shekara 7 batare da wata ishash-shiyar kulawa ba. Mai gabatar da kara Badamasi Ya'u Gawuna shine ya karanto kunshin tuhumar, inda ya shaidawa kotu cewa, Ibrahim Aliyu da Fatima Lawan sun hada baki da matarsa, inda suka  Daure Namam mai shekaru 32 har na tsawan shekara 7 a daki. Idan zaku tuna 'yan sanda a jihar kano a ranar 13 ga watan Ogusta sun ceto Ahmad Aliyu Namama bayan samun bayanai daga wata Mazauniyar garin Farawa mai suna Rahama Muhammad, wacce ta labartawa 'yan sanda da kungi...