fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: JAMB

JAMB ta bayyana ranar rubuta jarabawar shekarar 2021

JAMB ta bayyana ranar rubuta jarabawar shekarar 2021

Ilimi
Fabian Benjamin, Kakakin JAMB ya bayyana cewa kowane dalibi dolene ya gabatar da lambar katin zama dan kasa a wajan yin Rijista   Yace akwai gurare 700 akasarnan da za'a iya yin rijistar kuma akwai jadawalinsu a kowane Ofishin JAMB da kuma shafin hukumar na yanar gizo.   Yace za'a fara rijistar JAMB din April 8 a kare a May 15 2021. Yace kuma ba zaa kara ranar yin rijistar ba.   Yace za'a rubuta jarabawar daga ranar 5 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan. “This is mandatory for participation in the 2021 registration exercise,” he said. “Registration will take place in 700 centres across the country; the list is available in all the state offices of JAMB and on its website at www.jamb.gov.ng.   “The approved schedule for registration and exami...
JAMB ta fitar da sanarwa ta Musamman kan jarabawar 2021

JAMB ta fitar da sanarwa ta Musamman kan jarabawar 2021

Ilimi
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga jami'a ta JAMB ta bayyana cewa, bata fitar da ranar Rubuta Jarabawar ta shekarar 2021 ba.   Tace dan hakane ma take kira ga dalibai da su yi watsi da bayanan dake yawo a shafukan sada zumunta kan Jarabawar.   Tace idan Lokacin rijistar yayi zata sanar da jama'a kamar yanda ta Saba.   This is to inform the general public that no date has been fixed for 2021 UTME registration. Kindly disregard any tweet from a fake account that stated otherwise.   “The general public will be duly informed when the date is fixed. Thank you.
JAMB ta sake tsayar da ranar da zata fara aiki  bayar da Admission

JAMB ta sake tsayar da ranar da zata fara aiki bayar da Admission

Uncategorized
Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a ta JAMB ta sanar da ranar 7 ga watan Satumba a matsayin ranar da zata fara aikin bayar da Admission ga sabbin Dalibai masu shiga jami'a.   JAMB ta dauki wannan mataki ne bayan da ta yi hanawa da shuwagabannin jami'o'i a yau. Tace ta dauki wannan mataki me dan baiwa dalibai da zasu rubuta jarabawar kammala Sakandare damar samun sakamakon jarabawarsu. Shugaban JAMB, Ishaq Oloyede ne ya tabbatar da hakan bayan kammala taron.
JAMB zata zauna dan tattauna maganar Admission a yau

JAMB zata zauna dan tattauna maganar Admission a yau

Siyasa
Hukumar dake kula da bada Admission na shiga jami'o'in Najeriya, JAMB ta bayyana cewa a yau, Litinin zata zauna da masu ruwa da tsaki dan fitar da sabuwar ranar fara aikin baiwa Sabbin Dalibai Admission din.   JAMB a baya a irin wannan zama da ta yi ta bayyana ranar 22 ga watan Augusta a matsayin ranar da zata fara bayar da Admission. Saidai saboda yanda gwamnati ta tsara cewa za'a yi jarabawar kammala sakandare a ranar 17 ga watan Augusta, JAMB din ta yanke shawarar dage fara aikin samarwa da dalibai Admission din saboda da yawansu da suka rubuta jarabawar basu da sakamakon kammala Sakandare a hannunsu.
Daliban da suka yi fice a JAMB ta bana sun samu kyautar Miliyan 16

Daliban da suka yi fice a JAMB ta bana sun samu kyautar Miliyan 16

Siyasa
Matashiyar nan da ta samu maki mafi yawa a jarabawar Shiga jami'a ta JAMB, Egoagwuagwu Agnes Maduafokwa ta samu gagarumar kyauta kan bajintar data yi. Yarinyar da 'yar Asalin jihar Anambra ce ta samu maki 365 ckin jimullar maki 400 na jarabawar kamar yanda muka kawo muku a baya. Da ita da sauran dalibai 16 da suka fi samun maki da yawa, kungiyar kwararrun Injiniya ta kasa, Karkashin shugabanta, Babagana Mohammed sun karramasu da jimullar Naira Miliyan 16, watau kowannensu Naira Miliyan 1 kenan.
Hoton Dalibar data fi yawan Maki a Jarabawar JAMB ta 2020

Hoton Dalibar data fi yawan Maki a Jarabawar JAMB ta 2020

Uncategorized
Hukukar Shirya jarabawar Shiga jami'a ta JAMB ta bayyana sunayen dalibai 10 da suka fi yawan maki a jarabawar wannan shekarar ta 2020.   Daga ciki an samu dan Arewa 1 daya fito daga jihar Kwara, kamar yanda muka kawo muku a baya.   Wadda ta samu maki mafi yawa daga jihar Anambra ta fito me suna Egoagwuagwu Agnes Maduafokwa. Ta ci maki 365 daga jimullar maki 400 da ake dashi a jarabawar.   Tana son yin karatu a jami'ar University of Ibadan.
JAMB ta bayyana dalilin da zai sa dalibai Miliyan 1.3 ba zasu samu shiga jami’a ba a shekarar 2020

JAMB ta bayyana dalilin da zai sa dalibai Miliyan 1.3 ba zasu samu shiga jami’a ba a shekarar 2020

Uncategorized
Akwai yiyuwar cewa dalibai Miliyan 1.3 da suka rubuta jarabawar shiga jami'a  ta JAMB ba zasu samu gurbin karatu ba a shekarar 2020.   Wannan kuwa zai farune saboda daliban sun bayyana cewa basu da sakamakon kammala Sakandire yayin rijistar JAMB. WAEC da NECO wanda ya kamata a rubutasu a watannin Mayu da Afrilu ba'a samu Rubutawa ba saboda zuwan Annobar cutar Coronavirus/COVID-19.   JAMB ta bayyana maki 160 a matsayin wanda za'a dauki daliban jami'o'i dashi da kuma Maki 120 a matsayin wanda za'a dauki daliban kwalejojin Ilimin kimiyya dashi.   Ta kuma bayyana cewa zata fara aikin samar da Guraben karatu ga daliban da suke da sakamakon kammala Sakandire a watan Augusta me zuwa.   Rijistaran JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa sai id...
JAMB ta bayyana jami’o’in da sai mutum na da maki 200 sannan zasu bashi Adimishon

JAMB ta bayyana jami’o’in da sai mutum na da maki 200 sannan zasu bashi Adimishon

Uncategorized
Duk da bayyana cewa makin jarabawar JAMB 160 ne dalibai ke bukata a shekarar 2020 kamin su samu Admishon a jami'o'in kasarnan, JAMB ta bayyana cewa akwai jami'o'in da sai mutum na da maki 200 sannan zasu bashi Admishon.   Jami'o'in sune, University of Lagos, University of Ibadan, Covenant University, Obafemi Awolowo University and University of Benin, kamar yanda shugaban dake kula da watsa labarai na JAMB din, Dr. Fabian Benjamin ya bayyana.   Hakanan yace akwai Jami'o'in da sai mutum na da maki 180 sannan zai samu Admishon wanda suka hada da: Lagos State University (190); Afe Babalola University (180), Nigerian Army University, Biu (180); University of Jos (180), University of Abuja (180), Redeemers University (180), University of Ilorin (180), Ahmadu Bello Universi...
Da Dumi-Dumi:JAMB ta bayyana 160 a matsayin makin da dalibai ke buta domin shiga jami’a na shekarar 2020

Da Dumi-Dumi:JAMB ta bayyana 160 a matsayin makin da dalibai ke buta domin shiga jami’a na shekarar 2020

Uncategorized
JAMB a ranar talata, ta amince da maki 160 ko sama da haka a matsayin makin shiga jami'o'in gwamnati na shekarar 2020 na kasa. Hukumar ta JAMB ta cimma matsayar ne a babban taron na 20 kan shiga makarantun gaba da sakandare a Najeriya wanda aka yi a Abuja. Hukumar ta kuma amince da maki 140 a matsayin mafi karancin makin UTME don shiga cikin jami'o'i masu zaman kansu.
Da Dumi-Dumi: JAMB zata bayyana yawan Makin da Dalibai ke bukata wajan shiga jami’a a Yau

Da Dumi-Dumi: JAMB zata bayyana yawan Makin da Dalibai ke bukata wajan shiga jami’a a Yau

Uncategorized
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar shirya jarabawar shiga Jami'a ta JAMB a yau dinnan,Talata, 16 ga watan Yuni ake tsammanin zata bayyana yawan makin da Dalibai ke bukata kamin shiga jami'a da ake kira da Cut-off marks a turance.   Hakan ya bayyanane a sanarwar da JAMB din ta fitar ta shafinta na yanar gizo inda ta bayar da hakuri kan rashin sanar da zaman da yanzu haka ta ke yi da masu ruwa da tsaki na bangaren ilimi dan samo hanyar ci gaba ds karatun zangon shekarar nan. A cikin taronne za'a tattauna yanda za'a ci gaba da karatu da kuma yawan makin da dalibai ke bukata kamin su shiga jami'a.   Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajuiba ya bayyana a cikin taron cewa kada wanda ya bude makarantu har sai gwamnatin tarayya ta bada izinin yin hakan.   ...