
Tsohon Gwamnan Adamawa, Ngilari ya bar PDP zuwa APC
Tsohon gwamnan Adamawa, James Ngilari ya koma jam'iyyar APC daga PDP.
Shugaban jam'iyyar a Jihr, Ibrahim Bilal ne ya bayyana haka ga manema labarai a Yau, Asabar a Yola.
Ya kara da cewa Ngilari ya gaya masa cewa ba dan neman wani Mukami ne yasa ya koma APC ba kawai dai ya komane dan samun 'yancin Siyasa, sannan ya koma jam'iyyar ne tare da magiya bayansa.