fbpx
Friday, May 27
Shadow

Tag: Jami’a

Jami’o’in Najeriya sun shirya komawa Karatu>>Inji Wata Kungiyar Malamai

Jami’o’in Najeriya sun shirya komawa Karatu>>Inji Wata Kungiyar Malamai

Uncategorized
Wata kungiyar malaman jami'a me suna CONUA ta bayyana cewa jami'o'in Najeriya sun shirya tsaf dan komawa karatu.   Kunngiyar a sanarwar data fitar Ranar Asabar bayan taron masu ruwa da tsaki tace makarantun sun shirya komawa, gwamnati suke jira. Hutudole ya samo muki daga Rahoton kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN cewa CONUA ta balle daga kungiyar malaman jami'a ta ASUU ne bayan da aka samu rashin jituwa. Kungiyar tace gwamnati ta samar da kayan aiki da zasu baiwa malamai da dalibai kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus/COVID-19.  Hutudole ya fahimci kungiyar tace cutar Coronavirus/COVID-19 da wuya ta tafi nan kusa dan hakane ma bai kamata a dakatar da harakar makarantu gaba daya ba saboda cutar.
ASUU Ta tafi Yajin Aikin Gargadi Na Sati Biyu

ASUU Ta tafi Yajin Aikin Gargadi Na Sati Biyu

Siyasa
Kungiyar Malaman Jami'oi (ASUU) a ranar Litinin ta ayyana wani yajin aiki na sati biyu don nuna rashin amincewa da rashin biyan albashin malamai.   Shugaban kungiyar na kasa Biodun Ogunyemi ne ya baiyana hakan bayan taron majalisar zartarwa ta ASUU a Enugu.   Ya ce matakin yajin aikin shi ne tilastawa gwamnati aiwatar da yarjejeniya da kuma kudurin amincewa da ta yi da kungiyar daga shekarar 2009, 2013, 2017 da kuma 2019.