
Jami’ar Maryam Abacha ta bayar da kyautar Naira milliyan N1m ga Dalubar data samu maki mafi kyau a Jami’ar
Hukumar kula da Jami’ar Maryam Abacha dake Jamhuriyar Nijar (MAUUN), Maradi, ta bayar da kyautar Naira miliyan 1 ga dalibar data kammala karatun digiri ta kuma samu maki mafi kyau a jami’ar.
Maryam Abdullahi wanda ta fito daga jihar Kano, ta samu sakamako na farko wato First Class a fannin Shari'a dake jami'ar.
Kakakin jami’ar, Ali Kakaki ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Kano.
A lokacin da yake gabatar da kudin tallafin karatun digiri na biyu ga dalubar Shugaban jami'ar Farfesa Adamu Gwarzo, ya bukuaci Dalubai da su mai da hankali da kuma nanu kwazo a kan karatunsu.
Jami'ar ta gabatar da wannan tallafin ne ga Daluba Maryam Abdullahi a wata liyafa da a ka shirya ga daluban da suka kammala karatun digiri a jami'ar