
Leicester City ta dare saman teburin Premier League bayan lallasa Wolves da 1-0
Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta lallasa Wolverhampton Wanderers da ci 1-0 a wasan gasar Premier League da suka buga da yammacin yau, Lahadi.
Jamie Verdy ne ya ciwa Leicester City kwallo a bugun Penareti wanda kuma ya sake samun wani bugun amma ya barar.
Wannan yasa Leicester City ta dare saman teburin gasar Premier League. A yanzu Verdy babu kungiyar dake buga gasar Premier League da bai ci kwallo ba.