
Bidiyon yanda aka kama ma’aikacin Ofishin jakadancin Najeriya dake Kasar Jamus Turmi da Tabarya da wata mata saboda ya sabunta mata Visa, An dakatar dashi daga aiki
A jiyane Bidiyo ya bayyana inda aka ga babban jami'i tsaro na ofishin jakadanci Najeriya dake kasar Jamus an kamashi turmi da tabarya yana lalata da wata mata.
An yi zargin cewa ya dade yana lalata da mata dan ya sabunta musu Visa. Bidiyon ya watsu sosai a shafukan sada zumunta.
A martaninsa, Ofishin jakadancin Najeriya dake Jamus din ya sanar da dakatar da wannan ma'aikaci.
Jakadan Najeriya a kasar Jamus, Yusuf Tuggar ya bayyana a sanarwar cewa basu lamuntar cin zarafi kowane iri kuma suna binciken lamarin.
Yace idan aka gama binciken za'a hukunta me laifi.
https://twitter.com/JustSociety4all/status/1328472402972565504?s=19
“We have a zero-tolerance policy towards abuse of office and especially of sexual misconduct. Our full ...