fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Tag: Janar Sani Abacha

An dawowa da Najeriya Dala Biliyan 2.4 na Abacha

An dawowa da Najeriya Dala Biliyan 2.4 na Abacha

Siyasa
Lauya Enrico Monfriti wanda gwamnatin tarayya ta dauka aiki dan ya taimaka a dawo mata da kudaden da ake zargin tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha ya sata, ya bayyana cewa zuwa yanzu an dawowa da Najeriya Dala Biliyan 2.4 na tsohon shugaban kasar.   Saidai akwai wata Dala Miliyan 192 data makale a bankunan UK, Faransa da kuma Jersey.   Lauyan ya bayyana hakane a hirar da BBC ta yi dashi. A shekarar 1999 ne ya fara wannan aiki nasa kuma yana da kaso 4 cikin 100 na kudaden da ake katowa. However, another $192million is locked up in accounts in UK, France and Jersey.   According to Monfrini, $30m of the money is sitting in the UK to be returned, $144m is in France and a further $18m in Jersey.
Janar Buratai ya zarta Janar Sani Abacha inda ya zama shugaban sojojin Najeriya da ya fi dadewa akan Mulki

Janar Buratai ya zarta Janar Sani Abacha inda ya zama shugaban sojojin Najeriya da ya fi dadewa akan Mulki

Siyasa, Uncategorized
Janar Tukur Yusuf Buratai wanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sauke a jiya daga mukami  shugaban sojojin Najeriya ya kwashe watanni 66 akan wannan mukami.   Hakan tasa ya zama shine shugaban sojojin Najeriya da ya fi dadewa akan wannan mukami. Kamin shi, marigayi janar Sani Abacha ne yafi dadewa inda ya kwashe watanni 60 rike da wannan mukami.   Na 3 da ya fi dadewa shine David Ejoor me watanni 56, sai kuma TY Danjuma me watanni 51, sai Azubuike Ihejirika me watanni 40.  
Gwamnatin Tarayya ta zabi kungiya mai zaman kanta domin sanya ido kan yanda za’a kashe dala miliyan 311 na Abacha

Gwamnatin Tarayya ta zabi kungiya mai zaman kanta domin sanya ido kan yanda za’a kashe dala miliyan 311 na Abacha

Siyasa
Gwamnatin Tarayya ta zabi kungiyar farar hula, CLEEN, don sanya ido kan kashe kashin karshe na dala miliyan 311 da aka dawo da su wanda marigayi Shugaban kasa, Janar Sani Abacha ya wawure, in ji Ofishin Babban Lauyan Tarayya. ranar alhamis. Kudin, wanda aka dawo da su a watan Fabrairun wannan shekara, an ce an ware su ne don wasu manyan ayyuka guda uku - Gadar ta biyu ta Niger, Babbar hanyar Abuja zuwa Kano da kuma Babban titin Legas zuwa Ibadan. Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga AGF, Dakta Umar Gwandu, ya ce "makasudin shigar da kungiyar ta CSO shi ne don kara nuna gaskiya wajen gudanar da kudaden da aka gano". Ya ce amincewa da gidauniyar CLEEN don gudanar da sa ido kan yadda aka kashe kudaden ya zo ne bayan gabatarwar da Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, A...
Ina kasar Amurka aka gargadeni idan na dawo gida Abacha zai kamani kuma kasar ta bani mafakar siyasa amma naki na Dawo>>Obasanjo

Ina kasar Amurka aka gargadeni idan na dawo gida Abacha zai kamani kuma kasar ta bani mafakar siyasa amma naki na Dawo>>Obasanjo

Siyasa
Tsohon shugaban kasa, Chief Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a lokcin mulkin tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha,  ya je wani taro kasar Amurka, marigayi, jakadan Kasar Amurka a Najeriya, Mr. Walter Carrington ya bayyana masa cewa idan ya dawo Najeriya za'a kamashi.   Obasanjo ya bayyana hakane a wasikar da ya aikewa matar Marigayin ta ta'aziyya inda ya bayyanashi a matsayin wani gwarzo. Hutudole ya fahimci Walter ya baiwa Obasanjo damar samun mafaka a kasar Amurka dan kada ya dawo gida Obasanjo ya kamashi. Saidai Obasanjo ya bayyana duk da wannan ta yi amma yaki ya dawo gida kuma gwamnatin Abacha ta kamashi ta daure. Hutudole ya tattaro muku yanda Obasanjo ya bayyana Walter a matsayin mutumin kirki wanda yace koda bayan da yake kulle a gidan yari, Marigayin ya rika ...
Kasar Ireland zata dawowa da Najeriya wasu kudin Abacha

Kasar Ireland zata dawowa da Najeriya wasu kudin Abacha

Siyasa
Kasar Ireland zata dawowa da Najeriya kudaden da tsohon shugaban kasa, Marigayi Sani Abacha ya kai bankin kasarta.   Tsohon shugaban kasar da ya mulki Najeriya daga shekarar 1993 zuwa 1998 an ti ta dawo da kudaden da ya kai kasashen waje tun bayan da ya mutu. Hutudole ya fahimci wadannan kudade na kasar Ireland da za'a dawo dasu sun kai Yuro Miliyan 5.5. Kwatankwacin wadannan mudi a Naira sun fi Biliyan 2. Ministan shari'a ta kasar Ireland din, Helen Mcentee ta bayyana cewa zasu dawowa da Najeriya kudadenne saboda girmama dokokin kasa da kasa.   Hutudole ya ruwaiti muku cewa a shekarar 2014 ne aka yi alkawari tsakanin Najeriya da kasar ta Ireland cewa za'a dawo mata da kudin.
“Abin kunya ne a yi wa mutumin da ya mutu karya” matar Abacha ta yi magana a kan kudaden Abacha

“Abin kunya ne a yi wa mutumin da ya mutu karya” matar Abacha ta yi magana a kan kudaden Abacha

Siyasa
Maryam, matar tsohon shugaban mulkin soji, marigayi Sani Abacha, ta ce abin kunya ne a yi wa mijinta karya akan batun kudadin sata da aka danganta da shi.   A wata hirar da aka yi don bikin tunawa da cika shekaru 22 da rasuwarsa, Maryam ta fada wata majiya, cewa gaskiya game da kudaden da aka dawo da su wanda ke da alaka da mijinta zai bayyana nan bada dadewaba. Matar ta zargi manyan Kano da cin amanar mijinta, wanda ya mutu a shekarar 1998, duk da "irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban jihar da kasa baki daya". Ta bayyana tsohon mijinta a matsayin mutumin da ya taimaka wa mutane da yawa. Ta ci gaba da cewa "Ya yi aiki a Kano kuma ya kafa mutanen Kano, amma akwai mutanen da ya taimaka da yawa amma har yanzu ba su gaishe ni, ba gaira babu dalili." Kudade ...
Abacha ya ajiye kudi a kasashen waje don kada ‘yan Najeriya su wahala>> Majo Al-Mustapha

Abacha ya ajiye kudi a kasashen waje don kada ‘yan Najeriya su wahala>> Majo Al-Mustapha

Siyasa
Majo Hamza Al-Mustapha ya ce marigayi Janar Sani Abacha, Shugaban mulkin soja wanda ya mutu a shekarar 1998, ya ajiye kudi a kasashen waje don kada ‘yan Najeriya su sha wahala. An dawoda sama da dala biliyan 3.624 da Abacha ya sata zuwa kasashe hudu tsakanin 1998 da 2020. A watan da ya gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce an sace kusan dala biliyan 1 a karkashin Abacha. A lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar alhamis, Al-Mustapha, wanda ya kasance babban jami’in tsaro na Abacha, ya ce kudaden da aka tara a bankunan kasashen waje a lokacin mulkin wani hukunci ne na gama gari da ya shafi manyan masu ruwa da tsaki. "Na ce akwai lokacin da za a sanya takunkumi a Najeriya. Don haka akwai shirye-shirye na ajiye kudi a kasashen waje domin Najeriya da 'yan Najeriya ...
Sau 8 aka yi yunkurin yi wa Abacha juyin mulki>>Al-Mustapha

Sau 8 aka yi yunkurin yi wa Abacha juyin mulki>>Al-Mustapha

Siyasa
Tsohon babban mai dogarin marigayi janar Sani Abacha, Hamza Al-Mustapha, ya ce sau takwas ana yunkurin yi wa tsohon shugaban kasar juyin mulki. "Kafin lokacin da ya rasu, ana shirin yi masa juyin mulki na takwas ne amma 'yan Najeriya su suni cewa an yi masa yunkurin juyin mulki na uku ne amma gaskiyar magana ita ce guda takwas ne aka yi, a kan na takwas din ne ya rasu," in ji Al-Mustapha a hirarsa da BBC a dai-dai lokacin da marigayi Abacha ya cika shekara 22 da rasuwa. Al-Mustapha ya ce akwai gyara daga rahotannin da ake zargin cewa kudin da ake mayar da su Najeriya na tsohon shugaban ne. Ya ce wadannan kudade mallakar gwamnatin Najeriya da shugabannin al'ummar kasar su ka amince a ajiye su a asusun kasashen waje ne.
Ba a kula da mu tun bayan rasuwar mahaifinmu>>Iyalan Abacha

Ba a kula da mu tun bayan rasuwar mahaifinmu>>Iyalan Abacha

Siyasa
Shekaru ashirin da biyu bayan rasuwar tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Janar Sani Abacha, iyalansa sun bayyana yadda suke ji dangane da maraici.     Daya daga cikin 'ya'yan marigayin, Sadiq Abacha, ya shaida wa BBC cewa alakarsu da wasu abokan mahaifinsu a yanzu tana ba su mamaki.     Sadik ya ce, "Kamar iyalan janar Babangida ana gaisawa ana kuma mutunci, haka iyalan shugaban kasa na yanzu Muhammadu Buhari suma ana gaisawa".     Ya ce idan sun hadu ana gaisawa a yi dan labari sannan a dan tuna da baya amma da iyalan janar Babangida ake hakan.     Sadik ya ce, a bangaren iyayen nasu kuwa a gaskiya sun zaci cewa bayan rasuwar mahaifin nasu za a dan jasu a jiki a rinka basu shawara ko makamancin haka, amma sam ...
Mutuwar Abacha babban rashin ne ga Najeriya, Allah ne kawai zai saka mai kan ayyukan da yayi>>Manjo Al-mustapha

Mutuwar Abacha babban rashin ne ga Najeriya, Allah ne kawai zai saka mai kan ayyukan da yayi>>Manjo Al-mustapha

Siyasa
Tsohon shugaban tsaro na mariganyi manjo janar, Sani Abacha,  manjo Al-Mustapha, yace najeriya tayi babban rashin shugaba. Al-Mustapha Wanda ya fada haka a Kano gurin tunawa da shekaru 22 bayan mutuwar shugaba Abacha. Yace wanda suka kaima shugaban hari suna nuna bangaran shi marar kyau kuma da buye kyawawan ayyukanshi. Yace Allah ne kawai zai sakama shugan da abubuwan dayayima kasan nan kuma baza a taba mantawa dashi ba kuma har wanda ba'a haifaba zasu amfana da abubuwan da yayi. Daga karshe yace Abacha yasamu dala miliyan 200 ne kawai a asusun kasa amma yayi amfani da su gurin farfadu da kasan kuma yace a lokacin Abacha an saida dala a nera 85 kuma kasuwanci ya habbaka a wancan lokacin.