fbpx
Thursday, July 2
Shadow

Tag: Janar Tukur Yusuf Buratai

“Ba Za Mu yi Sulhu Da Yan Bindiga Ba”>>Shugaban Sojojin Kasan Najeriya, Laftanal Tukar Buratai

“Ba Za Mu yi Sulhu Da Yan Bindiga Ba”>>Shugaban Sojojin Kasan Najeriya, Laftanal Tukar Buratai

Tsaro
Babban Hafsan Sojan, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi kakkausar suka ga duk wani yunkuri da yan siyasa suke yi na yin sulhu da yan bindigan, yana mai jaddada cewa, “Sojojin ba za su yi sulhu da su ba”. Da yake magana da manema labarai na Zamfara a garin Faskari na jihar Katsina kusa da jihar Zamfara a ranar Laraba, Buratai ya ce, Sojojin za su fuskance su sosai tare da kashe yan bindigan idan har suka kasa mika wuya amma ya soke hukuncin yiwuwar tattaunawa da su. "Za mu tabbatar da cewa mun yaki 'yan bindiga da sauran ayyukan ta'addanci a duk sassan kasar amma ba sassauci, kamar yadda nake kira ga yan bindiga da sauran masu laifi da su mika wuya tare da rungumi zaman lafiya." Buratai ya kara bayani game da ikirarin cewa Sojojin sun gaza a yakin da ake yi da masu tayar da
Yanayin da Najeriya ke ciki yafi na yakin basasa Muni>>Sarkin Daura

Yanayin da Najeriya ke ciki yafi na yakin basasa Muni>>Sarkin Daura

Tsaro
Me martaba sarkin Daura, Dr. Umar Farouk Umar ya bayyana damuwa kan halin matsalar tsaro da Jihar Katsina dama Arewa gaba da ya take ciki a halin yanzu inda ya bayyana abin da cewa yafi yakin basasa muni.   Sarkin ya bayyana hakane a yayin ziyarar da shugaban soji, Janar Tukur Yusuf Buratai ya kai masa a fada a ziyarar da yake a jihar Katsina. Sarki Umar ya jinjinawa Sojojin Najeriya bisa kokarin da suke wajan dakile matsalar tsaton inda ya gargadi mutane da su daina katsalandan kan harkar tsaro.   Yace shugaba Buhari ya gaji mulkin kasarnanne a lokacin da take kusa da rugujewa amma fa a matsayinshi na tsohon janar din soja kuma shugaban kasa har sau 2, yasan matsalar tsaron fiye da farar hula. Yace yawanci abinda mutane ke cewa a harkar tsaro irin abinnanne wa...
Baku da hujjar rashin samun nasara>>Buratai ya gayawa sojoji na Musamman da aka Kai Katsina

Baku da hujjar rashin samun nasara>>Buratai ya gayawa sojoji na Musamman da aka Kai Katsina

Tsaro
Shugaba sokojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai a ganawar da yayi da sojoji na musamman da aka kai jihar ya bayyana cewa basu da wata hujjar nuna gazawa.   Ya bayyana hakand a wani tarin cun abincin dare da aka shirya masa da sojojin inda yace su dage dan ganin an kawo matsalar tsaron nan ba da jimawa ba. Yace irin wannan hali da ake ciki shi yasa aka basu horo na musamman kuma yana fatan su kauda kai daga abubuwan karya da ake yadawa a shafukan sada zumunta dan su yi aikinsu yanda ya kamata, yace shugaban sojoji da Najeriya zasu rikawa aiki.   Yace shugaba Buhari ya gaya musu cewa ba lallai a wannan damunar manoma su samu zuwa ginakinsu ba amma ya bashi tabbacin cewa manoman zasu koma gonakinsu nan bada jimawa ba, yace yana fatan hakan zata tabbata. &nb...
Ya kamata a saki sojan da ya caccaki Buratai saboda Gaskiya ya fada, Buratai dan Kasuwane yanzu>>Dr. Junaid Muhammad

Ya kamata a saki sojan da ya caccaki Buratai saboda Gaskiya ya fada, Buratai dan Kasuwane yanzu>>Dr. Junaid Muhammad

Tsaro
Tsohon dan majalisa a jamhuria ta 2, Dr. Junaid Muhammad ya bayyana cewa ya kamata a saki Lance Corporal Martins da yayi bidiyo ya caccaki shugaban sojoji, Janar Buratai da sauran manyan jami'an tsaro.   Yace sojan Gaskiya ya fada kuma tsareshi da ake yi bai kamata ba. A wani bidiyo da muka kawo muku a baya, Lance Corporal Martins ya bayyana cewa Buhari,  Buratai da Monguno duk sun baiwa Arewa kunya ganin cewa daga yankin suka fito amma gashi duk da haka ana ta kashe mutane.   Yace zai kaisu kara kotun hukunta manyan Laifuka ta Duniya ICC, Saidai Rahotanni da suka bayyana daga baya sun ce an kama sojan.   Junaid yace Buratai kamar dan kasuwa ya koma a gidan soja kuma ya gaza a aikinshi na tsare Najeriya daga hare-hare inda yace idan ba'a saki wancan
Buratai ya bukaci janarorin soja su je fagen daga a fafata dasu

Buratai ya bukaci janarorin soja su je fagen daga a fafata dasu

Tsaro
Shugaban sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai a zaman ganawar da yayi da yayi da manyan sojoji a yau ya bukaci da su tabbata an aiwatar da umarnin shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gaggawa.   Yace janar-janar da kuma kwamandoji kada su rika zama a ofis, su fita suje filin daga inda ake yaki dan su tabbatar ana yin abinda ya kamata. Yace dole a canja tsarin yanda ake yakar 'yan Boko Haram da 'yan ta'adda dan ganin an kawo karshen su da gaggawa.   Sanarwar bayan taron ta bayyana cewa ranar soji da za'a yi, za'a yi ta ne a jihar Katsina dan tabbatar da tsaro.
Buratai ya jinjinawa Sojoji bisa tsayin daka da suka yi suka hana Boko Haram sakat a Monguno: Yace Katsinawa, Zamfarawa da Sakkwatawa su shirya yana nan zuwa dan maganin haukan da ‘yan Bindiga ke musu

Buratai ya jinjinawa Sojoji bisa tsayin daka da suka yi suka hana Boko Haram sakat a Monguno: Yace Katsinawa, Zamfarawa da Sakkwatawa su shirya yana nan zuwa dan maganin haukan da ‘yan Bindiga ke musu

Tsaro
Shugaban sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana jinjina ta ban girma ga dakarunsa bisa tsayin Dakar da suka yi a harin da Boko Haram/ISWAP suka kaiwa garin Monguno a jiya,Asabar.   Buratai a wata sanarwa da hedikwatar sojojin ta fitar yace ya ji matukar dadi bisa yanda sojojin suka wa Boko Haram Illa sosai a harin suka kuma kashe da dama daga cikinsu tare da kwace makamai. Yace yana bukatar kwamandan Rundunar Operation lafiya dole da yasa a kara kaimi wajan kakkabe duk wata matsugunin Boko Haram da aka samu a Borno.   Buratai ya bayyana cewa yana kuma amfani da wannan dama wajan baiwa mutanen Arewa maso gabas, musamman Sakkwato,  Zamfara da Katsina tabbacin cewa su jira yana nan zuwa dan maganin haukan da 'yan Bindiga ke musu.   Ya kara
Yayin da nake fagen yaki da Boko Haram, Sojoji da yawa a shirye suke su bada ransu akaina>>Janar Buratai

Yayin da nake fagen yaki da Boko Haram, Sojoji da yawa a shirye suke su bada ransu akaina>>Janar Buratai

Tsaro
Shugaban Sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai da yake a Arewa maso gabas ya bayyana cewa sojoji da dama suna shiga gaba suce zasu tare mai duk wani harsashi da za'a harbo. Ya bayyana hakane bayan ganawar da yayi da shugaban kasa,Muhammadu Buhari a fadarsa dake Aso Rock a yau, Litinin inda yace ya jene ya baiwa shugaba Buhari ba'asi akan abinda ke faruwa game da tsaron kasa da kuma mataki na gaba da za'a dauka.   Janar Buratai yace ya yaba sosai da jajircewar Jami'ansa a lokacin da yake tare dasu dan sukan tashi suce a shirye suke su tare masa harsashi.   Yace hakanan a yankin Arewa maso yamma sojojin Najeriya na iya bakin kokarinsu wajan ganin sun murkushe matsalar tsaron da ake fama da ita yace suna kara kai sojoji yankin.   Y...
Kimanin yan ta’addan Boko Haram 1400 ne muka kashe a Arewa Maso Gabas>>Buratai

Kimanin yan ta’addan Boko Haram 1400 ne muka kashe a Arewa Maso Gabas>>Buratai

Tsaro
Wannan daya daga cikin da daman nasarorin da sojojin Najeriya ke samu, kamar yadda shugaban sojojin Najeriya, Janar Tukur Buratai ya fada.     Shugaban sojojin, wanda ya kasance afilin daga da sojoji, ya fada haka bayan wani zama da sukayi da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Abuja. Janar Buratai ya bayyan jin dadin game da kwazon da sojojin suke nunawa, ya kara da cewa sojojin suna kara maida hankali dan su tabbatar sun fidda duk wani ta'addanci da fashi a kasarnan.
Ba zamu sake amincewa da tsoro, ko zagon kasa ba>>Janar Buratai

Ba zamu sake amincewa da tsoro, ko zagon kasa ba>>Janar Buratai

Siyasa
Shugaban sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya nanatawa sojojin cewa ba zasu amince da maganar tsoro ko zagon kasa ko kuma ragwangaka a aiki ba.   Buratai ya bayyana hakane a yayin da ya halarci wajan da ake baiwa sojojin horo akan yaki da kuma sarrafa sabbin kayan aikin da hukumar sojin ta siyo. Ya bayyana cewa, yaji dadin ganin yanda Sojojin ke daukar darasin da ake basu sannan kuma ya yaba da yanda masu horaswar suma suke aiki tukuru. Saidai ya gayawa sojojin cewa su kiyaye dan ba zasu dauki ragwanci, ko tsoro ba a wajan aiki.   Yace da irin kayan aikin da suke dasu yanzu to lallai babu wata matsalar taaro da ba zasu iya murkushe taba a kasarnan.