
An bayyana sunan wadanda suka baiwa ‘yan Bindiga kudi a Zamfara dan kada su saki dalibai mata na Jangebe
Dr. Sani Abdullah Shinkafi, shugaban jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) a jihar Zamfara ya zargi shugabannin jam’iyyar APC na jihar da bayar da naira miliyan 56 ga ‘yan fashi don kin sakin‘ yan matan Jangebe da aka sace.
Ya ce, manufar su ita ce zagon kasa na kokarin samar da zaman lafiya na Gwamna Bello Mohammed Matawalle.
Shinkafi, wanda ya kasance dan takarar gwamna na APGA a 2019 a jihar Zamfara, ya yi wannan zargin ne yayin ganawa da manema labarai.
"Don haka, na kalubalanci 'yan siyasa daga bangaren masu mulki da na jam'iyyun adawa da su bayyana lambobin wayarsu zuwa binciken tsaro tun da ina da yakinin cewa labarin da zai fito daga wannan tsari zai zama abin mamaki," in ji shi.
A cewarsa, binciken jami'an tsaro na wayoyin sirri na zababbu...