
Abu daya ne ya ke hanamu kai Sojoji mu murkushe ‘yan Bindiga>>Shugaba Buhari yayi Allah wadai da sace daliban Jangebe
Shugaba Buhari yayi Allah wadai da sace dalibai Mata a Jangebe ta jihar Zamfara.
A sanarwar da ya fitar shugaban yace babu wani me laifi da ya fi karfin Gwamnati.
Yace dalili daya dake hana Gwamnatin daukar mataki akan 'yan Bindigar shine saboda kada a kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba. Yace za'a iya kai Tarin Sojoji kauyukan da ake wannan sace-sace amma abu daya ne ke takawa Gwamnati Birki shine kada a kashe wanda akale tsare dasu da kuma wanda basu ji ba basu gani ba.
Yace maganar garkuwa da mutane abu ne me matukar Hadari wanda yana Bukatar a bishi a sannu sannan a yi hakuri dan a samu a kubutar da wanda aka sace ba tare da an ji musu rauni ko mummunan kisa ba.
Yace 'yan Bindigar kada su taba Tunanin cewa sun fi karfin Gwamnati ...