
Watanni 3 bayan sakin wakar Jarumar Mata ta Hamisu Breaker an kalle ta sau Miliyan 3 a YouTube
Tauraron mawakin Hausa, Hamisu Breaker da tauraruwarsa ke kan haskakawa na kara samun karbuwa sosai a wajen jama'a.
Watanni 3 bayan sakin wakarsa ta jarumar Mata a shafinsa na YouTube, a yanzu wakar ta kerewa sa'a inda aka kalleta sama da Sau Miliyan 3.
https://m.youtube.com/watch?v=PsRn4s1Ygj8
Wakar ta Hamisu Breaker itace ta farko ta Hausa da aka kalleta da yawa haka a shafin na YouTube, wakar Hamisu Breaker ta Na yi Sa'a ce ta 2 da aka fi kallo da Miliyan 2.7 sai kuma So na Amana ta Garzali Milko me amiliyan 2.6.