
Jeff Bezos ya doke Elon Musk inda ya sake zama wanda ya fi kowa kudi a Duniya
Jeff Bezos ya kwace kambun me kudin Duniya daga hannun Elon Musk, baya Makonni 6.
Musk ya tafka Asarar dala Biliyan 4.5 bayan da darajar kamfaninsa na Tesla ya fadi da kaso 2.4 kamar yanda Bloomberg ta bayyana.
Shima Bezos yayi Asarar amma bata kai ta Musk ba inda shi Asarar Dala Miliyan 372 yayi. A yanzu, Bezos na da dala Biliyan 191 yayin sa Musk ke da Biliyan 190.