fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Jigawa

Wasu dai fatansu su ga shugaba Buhari da Tinubu sun bata, kuma hakan ba zai faru ba>>Gwamna Badaru

Wasu dai fatansu su ga shugaba Buhari da Tinubu sun bata, kuma hakan ba zai faru ba>>Gwamna Badaru

Siyasa
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya musanta rashin jituwa tsakanin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmad Tinubu. A hirarsa da Channelstv, Badaru ya bayyana cewa, an kawo labarin ne kawai dan saka rudani tsakanin mutane.   A Baya dai, hutudole.com ya kawo muku Rahoton cewa, Gwamna Badaru yace ba ba'a taba shugaba kamar Buhari ba Badaru yace mutane na son ganin an samu Baraka tsakanin Shugaba Buhari da Tinubu amma burinsu ba zai cika ba. Yace APC tsintsiyace madaurinki daya.   “I think people wanted to see that and that will not happen. I believe it is all politics. President Muhammadu Buhari, Bola Tinubu and all the leaders of the party speak with one voice.   “We have pushed that story about President Bu...
An kama dan shekaru 70 da yawa me shekaru 7 fyade a Jihar Jigawa

An kama dan shekaru 70 da yawa me shekaru 7 fyade a Jihar Jigawa

Tsaro
Jami'an tsaro sun kama wani dan shekaru 70 da zargin yiwa karamar yarinya me shekaru 7 fyade a jihar Jigawa.   Wanda aka kama din sunansa Ibrahim Nasaleh dake karamar hukumar Kiyawa. Kakakin 'yansandan jihar, Zubairu Ismail ya tabbatar da faruwar lamarin.   Yace an kai yarinyar da akawa fyaden Asibiti sannan kuma an kama wanda ake zargi. “The arrest was due to a report made by the mother of the victim who lives in Shuwarin Village,  Kiyawa Local Government at the Divisional Police Headquarters, Kiyawa, that the said Ibrahim Nasaleh had carnal knowledge of her daughter who is just seven years of the same address in his house. “The victim was quickly rushed to Sexual Assault Referral Center, Dutse for medical examination, while the case is still under investig...
Hoton Yanda akawa Gwamnan Jigawa Rigakafin Coronavirus/COVID-19 yana cikin Firgici ya dauki Hankula

Hoton Yanda akawa Gwamnan Jigawa Rigakafin Coronavirus/COVID-19 yana cikin Firgici ya dauki Hankula

Kiwon Lafiya
An yiwa Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badadu Abubakar rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19 a fadarsa dake Dutse.   Likitan Gwamnan ne ya masa Allurar. An kaiwa jihar ta Jigawa Rigakafi 68,520 kuma Gwamnan yace za'a kaisu cibiyoyin bada agajin Lafiya matakin farko dake bangarorin jihar Daban-daban.   Yace rigakafin bashi da illa. “We are going to distribute the vaccine to all the primary Health cares centres in 287 ward that was already been provided with steady power supply”
Gwamnatin Jigawa ta amince da daurin shekaru hudu ga masu daukar nauyin ‘yan daba na siyasa

Gwamnatin Jigawa ta amince da daurin shekaru hudu ga masu daukar nauyin ‘yan daba na siyasa

Tsaro
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da daurin shekaru hudu ga ‘yan siyasar da ke daukar nauyin’ yan bangar siyasa. Babban lauyan gwamnati, Musa Adamu Aliyu ya bayyana haka lokacin da yake yi wa manema labarai bayani game da cin zarafin dokar mutane. An ruwaito cewa Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya sanya hannu kan kudirin don zama doka. Gwamnan ya ce an sanya hannu kan kudirin don zama doka don kare hakkin masu karamin karfi a cikin al’umma. Adamu ya bayyana cewa Gwamnatin ta lura da yadda 'yan siyasa ke lalata makomar matasa ta hanyar amfani da su a matsayin barandan siyasa. “Abubuwan da dokar ta tanada sun hada da; Hukuncin kisa ga maza ko mata masu fyade ko kuma hukuncin ɗaurin rai da rai ba tare da zaɓi na tara ba ” "A dokar, amfani da 'yan daba...
Gwamnan Jihar Jigawa ya sakawa dokar daurin rai da rai da kuma kisa kan masu fyade da satar mutane hannu

Gwamnan Jihar Jigawa ya sakawa dokar daurin rai da rai da kuma kisa kan masu fyade da satar mutane hannu

Uncategorized
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya amince da dokar da majalisar jihar ta yi kan masu fyade da satar mutane dan kudin fansa.   Dokar ta tanadi hukuncin kisa ko kuma daurin rai da rai ba tare da bayar da damar biyan kudin diyya ba ga duk wanda aka kama da wadannan laifuka.   Gwamnan yace wannan doka zata rage aikata laifuka a jihar tasa kuma da amincewar  malamai da sauran masu ruwa da tsaki aka yi ta. The new laws stipulated in the bill include; Death sentence for male or female rapist or life sentence without the option of fine. Anyone who aides or gives order to rape another person shall receive a death or life sentence.”  
Hukumar Hisba ta lalata kwalaben giya 3000 a Jigawa

Hukumar Hisba ta lalata kwalaben giya 3000 a Jigawa

Tsaro
Hukumar Hisba ta jihar Jigawa ta lalata kwalaben giya 3000 da aka kwace a karamar hukumar Kazaure. Kwamandan karamar hukumar Malam Bello Musa Kazaure ya bayyana hakan bayan lalata giyar a Kazaure. Ya ce wannan matakin ya yi daidai da kokarin da rundunar ke yi na magance mummunar dabi'a da munanan halaye a tsakanin al'umma. Bello ya ce an kwace kwalaban giyar ne daga wasu gurare da ke garin Kazaure. Ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kamawa da gurfanar da duk wani mai siyar ko siyan giya a cikin Jihar. Ya ce wannan shi ne atisaye na biyar da jami'an rundunar ke gudanar wa a yankin don rage kaifin gani da ido a yankin. Bello ya lura cewa sha da sayar da giya sun kasance haramtattu a cikin jihar.
2023: Hotunan Wasu matasan Arewa suna nemi gwamnan Ebonyi ya tsaya takarar shugaban kasa

2023: Hotunan Wasu matasan Arewa suna nemi gwamnan Ebonyi ya tsaya takarar shugaban kasa

Siyasa
Wasu matasan Arewa sun nemi gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya tsayata takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.   Matasan sun fito ne daga jihar Jigawa, kuma sun bayyana masa hakane ne yayin da ya kai ziyarar aiki jihar ta Jigawa.   Matasan sun fito da yawa dauke da kwalaye masu kira ga gwamnan da ya fito takara saboda sun gamsu da aikin raya kasa da yake a jiharsa. Hutudole ya fahimci cewa gwamnan ya je jihar ne dan kaddamar da aikin titin garin Babura wanda gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya gina.   A yayin kadadamar da tititunan, Gwamna Umahi ya bayyana cewa APC tana aiki amma ba'a yayatasu yanda ya kamata. Ya jinjinawa Gwamna Badaru bisa ayyukan raya kasa. "We have served in various National assignments together and I have come to realiz...
Kotu tawa wanda aka samu da laifin Fyade daurin rai da rai a jihar Jigawa

Kotu tawa wanda aka samu da laifin Fyade daurin rai da rai a jihar Jigawa

Uncategorized
Babbar kotu a Dutse dake jihar Jigawa ta daure wani matashi daurin rai da rai, Sulaiman Ahmad dan kimanin shekaru 27 bisa laifin fyade.   Hakanan kotun ta daure wani data samu da laifin Fyade shima shekaru 21 sannan ta wanke wani ds aka yiwa zargi.   Premium times ta ruwaito cewa kakakin ma'aikatar Shari'a ta jihar, Zainab Baba Santali ce ta bayyana haka ga manema labarai a ranar Talata.   Ta bayyana cewa wanda aka yankewa Laifin, Ahmad dake kauyen Lutai na karamar hukumar Birnin Kudu ya aika laifinne ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2020. Kuma shaidu 4 sun bada shaida akan abinda ya aikata duk da cewa shi bai amsa laifinsa ba. Alkali Musa Ubale yace shaidun sun gamsar da kotu dan haka aka daure wanda ya aikata laifin daurin rai da rai a gidan yari.
Dan majalisar jihar Jigawa, Babban Bare ya rasu

Dan majalisar jihar Jigawa, Babban Bare ya rasu

Siyasa
Dan majalisar Jihar Jigawa, dake wakiltar Kafin Hausa, Hon Adamu Babban Bare ya rasu.   Shugaban kwamitin kula da yada labarai na majalisar, Hon. Aminu Zakari Tsubut ne ya bayyana haka inda yace sun kadu da samun labarin rasuwar abokin aikin nasu. Marigayin ya rasu yana da shekaru 57 bayan fama da rashin lafiya wadda ake zargin ciwon daji ne, kamar yansa Vanguard ta ruwaito.
Yarinya ‘yar shekaru 14 ta kashe kanta saboda mahaifin ta ya ki saya mata hijabi a Jigawa

Yarinya ‘yar shekaru 14 ta kashe kanta saboda mahaifin ta ya ki saya mata hijabi a Jigawa

Uncategorized
Wata yarinya ‘yar shekaru 14, Faiza Mustapha, ta rataye kanta har lahira a kauyen Maizogale da ke karamar hukumar Kiyawa a jihar Jigawa. Wani ganau ya fadawa jaridar DAILY POST cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a wani daji kusa da kauyen. Ya ce yarinyar ta yi amfani da igiya ta rataye kanta a kan bishiya don nuna bacin ranta game da rashin iyawar iyayen na siyan mata Hijabi. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce marigayiyar ta kashe kanta ne bayan da ta bukaci mahaifinta ya saya mata mayafin (Hijabi) wanda ya ki. Jinjiri ya ce wani mutum ne ya gano gawar a yankin kuma ya hanzarta sanar da jami'an tsaro. 'Yan sanda sun kara da cewa an kai yarinyar zuwa babban asibitin Dutse inda aka tabba...