
Da Dumi-Dumi:Gwamnan Jihar Delta da matarshi sun kamu da Coronavirus/COVID-19
Gwamnan Jihar Delta, Efeanyi Okowa da matashi sun kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.
Gwamnanne da kansa ya bayyana haka ta shafinshi na Twitter inda yace babu wata alamar damuwa a tare dasu kuma zasu ci gaba da killace kansu.
Yayi godiya ga mutane bisa addu'o'in da suke masa.
https://twitter.com/IAOkowa/status/1278268237231292419?s=19
A baya dai mun kawo muku yanda gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.