fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Jihar Edo

An sake kama fursunoni 3 da suka tsere daga gidajen yarin Edo da aikata laifin fashi da makami

An sake kama fursunoni 3 da suka tsere daga gidajen yarin Edo da aikata laifin fashi da makami

Tsaro
Jami'an rundunar 'yan sanda reshen jihar Edo sun sake tsare fursunoni uku da suka tsere daga cibiyoyin gyara biyu bayan wani hari da wasu' yan daba suka kai musu a yayin zanga-zangar ta ENDSARS, saboda fashi da makami. Wadanda ake zargin, Osamuyi Omoregbe, Raymond Aimua da Omon Ayo, suna daga cikin mutane 34 da ake zargi ‘yan sanda suka gabatar a hedkwatar rundunar a ranar Juma’a, 4 ga Disamba, saboda fashi da makami, satar mutane da kuma kungiyar asiri.   Da yake yi wa manema labarai bayani kan nasarorin da suka samu a yaki da laifuka a jihar, kwamishinan ‘yan sanda, Johnson Kokumon ya ce za a gurfanar da wadanda suka tsere din su uku saboda gujewa tsarewa da kuma sabon laifin da aka aikata.
Malamin jami’a ya kashe kansa a jihar Edo

Malamin jami’a ya kashe kansa a jihar Edo

Uncategorized
Ana zargin Wani malamin jami'ar Tayo Akpata dake jihar Edo, Friday Orobator ya kashe kansa ta hanyar rataya.   An gano gawarsa ne a bayan gidansa dake Birnin Benin da misalin karfe 1:30 na yammacin jiya, Juma'a. Shugaban kungiyar malaman jami'ar na jihar, Fred Omonuwa ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace Friday yayi ta korafi akan rashin kudi kamin ya kashe kansa.   Yace kamin ya kashe kansa ya rika gayawa na kusa dashi cewa ya gaji da rokon mutane dan samun kudin da zai kula da iyalansa sannan kuma ya kula da lafiyarsa gashi bashi da lafiya kuma bashi da kudin zuwa Asibiti.   Fred ya kara da cewa watanni 13 kenan suna bin gwamnati bashi amma da suka yi magana ance Siyasace.
Mu fa a jihar Edo bamu saka dala a aljihu>>Gwamna Obaseki ya gayawa Gwamna Ganduje

Mu fa a jihar Edo bamu saka dala a aljihu>>Gwamna Obaseki ya gayawa Gwamna Ganduje

Siyasa
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya mayarwa da takwaransa na jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje martani kan zargin da ya masa na cewa be wa mutanen jihar komai ba.   Ganduje a fadar shugaban kasa, bayan ganawa da shugaban, yace saboda gwamna Obaseki babu wani abin arzikin da ya tabukawa mutanen jiharsa, shiyasa zasu samu Nasara cikin sauki a zaben gwamna me zuwa.   Saidak Obaseki ta bakin magana da yawunsa ya bayyana cewa Gwamna Ganduje bashi da bakin da zai gayawa mai irin wannan magana koma wani gwamna a kasarnan.   Yace shi da yake da laifin karbar cin hanci, Duniya na kallonsa kiri-kiri. Yace yayiwa al'ummar jiharsa aikin da zasu gani su zabeshi.
CORONAVIRUS: Gwamnan Edo ya killace kan sa

CORONAVIRUS: Gwamnan Edo ya killace kan sa

Kiwon Lafiya
Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya killace kan sa tare da mika samfin din sinadaran jikin sa domin a yi gwaji, bayan yay i cudanya da Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugagab Kasa, wadanda dukkan su sun kamu da cutar.     Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Lbarai na Obaseki mai suna Crusoe Osagie ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa gwamnan ya killace kan sa tare da tura sinadarai domin a yi masa gwaji a gano shi shi ma ya kamu ko bai kamu din ba.     Ya ce “Gwamna ya killace kan sa, bayan ya cakudu da Gwamna Bala Mohammed da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, wadanda su biyun an tabbatar da cutar Coronavirus a jikin su.     Ya ce Obaseki ya gana da Bala ne a wurin taron gwamnoni...
Coronavirus/COVID-19: Mu ba zamu hana ayyukan addini ko rufe makarantu ba>>Gwamanatin jihar Edo

Coronavirus/COVID-19: Mu ba zamu hana ayyukan addini ko rufe makarantu ba>>Gwamanatin jihar Edo

Kiwon Lafiya
Gwamnan jihar Edo,Godwim Obaseki ya bayyana cewa a yanzu jiharsa ba zata dakatar da ayyukan Ibada ba ko kuma rufe makarantu ba.   Gwamnan ya bayyana hakane a jiya, Juma'a, 20 ga watan Maris na shekarar 2020 yayin da wasu shuwagabannin addinai suka ziyarshi.   Gwamnan yace gwamnatinsa ta dauki duk wasu matakai na ganin an dakile cutar. Ya ce akwai kuma shirye-shirye a kasa wanda idan cutar ta shiga jihar za'a kula da ita.   Jihohi da Dama irin su, Kaduna, Legas, Ekiti dadai sauransu sun dakatar da makarantu tmda tarukan ibada kkan cutar.