
Yan Bindiga sun kashe mutane biyar a jihar Kaduna
Wani mummunan lamari ya faru a ranar Lahadi a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna yayin da wasu ‘yan bindiga suka far wa kauyen Katarma da ke cikin karamar hukumar, inda suka kashe mutane biyar tare da jikkata wani mutum guda.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya ce ’yan bindigar sun far wa al’ummar ne da sanyin safiyar yau kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi wanda ya yi sanadin mutuwar mutanen biyar.
A wani lamarin, sojojin na 'Operation Safe Haven' sun ba da rahoton wani rikici tsakanin wasu matasa a ƙauyen Atuku na ƙaramar hukumar Jema’a, yayin da wani Afiniki Thomas ya samu mummunan rauni a goshinsa bayan da wasu matasa biyu suka far masa.
Daya daga cikin maharan, Sani Safiyanu...