
‘Yan bindiga sun kashe mutane 3, tare da sace mutane 9 a Katsina
Rahotanni daga jihar katsina na nuni da cewa wasu 'Yan bindiga sun kashe mutane 3, tare da yin garkuwa da wasu mata 9 a karamar hukumar Sabuwa da ke jihar Katsina.
Bincike ya nuna cewa ‘yan bindigar sun afkawa cikin kauyukan ne da daddare inda suka shafe tsawan kwana guda.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunan ta ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun kashe wani mai suna Ahmed Jabir da Abubakar, yayin da wasu mutane uku ke kwance a Asbiti cikim mawuyacin hali.
Wani mazaunin garin, Alhaji Muntari Musawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun isa gidansa da misalin karfe 1:30, suka tadda matarsa sannan sukai awon gaba da ita a kan babur.
Sai dai harzuwa wannan lokaci rundunara 'yan sanda basu ce komai ba.