fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Jihar Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi ta sha alwashin zakulo masu aikata laifi a jihar

Gwamnatin jihar Kebbi ta sha alwashin zakulo masu aikata laifi a jihar

Tsaro
Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Samaila Yombe Dabai mai (ritaya), ya sha alwashin cewa gwamnatin jihar zata zakulo masu aikata laifuka a cikin kungiyar 'Yan-Sakai wadanda ke fakewa suna aikata laifuka daban-daban a yankin Masarautar zuru. Dabai ya shaida hakan ne a yayin rangadin da ya gudanar a yankunan masarautar, A yayin da yake zantawa  da manema labarai a Birnin Kebbi, Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa wasu bata gari suna fakewa da aikin 'yan sintiri  suna aikata laifuka. A cewarsa Gwamnati ta gano hakan kuma tana shirin Daukan mataki domin dakile masu aikata miyagun laifuka a jihar.
Shugaban Karamar hukumar Kalgo a Jihar Kebbi ya rarraba kayan tallafi ga wadanda Ambaliyar ruwa ta Shafa A Jihar

Shugaban Karamar hukumar Kalgo a Jihar Kebbi ya rarraba kayan tallafi ga wadanda Ambaliyar ruwa ta Shafa A Jihar

Kiwon Lafiya
Shugaban karamar hukumar Kalgo A jihar Kebbi, Alhaji Samsu Umar Faruk ya kai kayan agaji da kudi zuwa ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa kwanakin baya a jihar. A cewarsa, ya kai taimakon ne domin ragewa al'ummomin da Ambaliyar ruwan ta shafa a yankin wahal-halu. Ya bayyana cewa sama da gidaje 156 ne ambaliyar ta lalata, a garuruwan Kalgo, Kirishi da Badariya. Fiye da mutane 60 da abin ya shafa za suci gajiyar tallafin kudi a Badariya yayin da mutane 96 za su amfana a garin Kalgo da kirishi da tallafin kudi naira dubu 14 ko wanan su. Hakimin Kalgo, Alhaji Haruna Bashar, ya yaba da gudunmawar da a ka baiwa al'ummar karamar hukumar.
Hotuna:A’isha Buhari ta aikewa wanda ambaliyar ruwa ya shafa tallafi a jihar Kebbi

Hotuna:A’isha Buhari ta aikewa wanda ambaliyar ruwa ya shafa tallafi a jihar Kebbi

Uncategorized
Uwargidan shugaban kasa,Hajiya A'isha Buhari ta aikewa wanda Ambaliyar ruwa ta shafa da kayan tallafi a jihar Kebbi.   Kayan tallafin da ta aika dasu sun hada da shinkafa, Man girki, kayan sawa, da Barguna. A'isha Buhari ta bayyana ta bakin kakakin ta Aliyu Abdullahi cewa, ta tausayawa wanda lamarin ya rutsa dasu musamman mata da kananan yara inda tace sauran guraren da lamarin Ambaliyar ruwan ya faru shima yana ranta.   Garuruwan da aka kai kayan tallafin sun hada da Kalgo, Bagudo, Zagga, Jega, Makera, Argungu.
Cikin shekaru 100 da suka gabata bamu taba ganin irin wannan Ambaliyar ruwan ba>>Jama’ar Kebbi

Cikin shekaru 100 da suka gabata bamu taba ganin irin wannan Ambaliyar ruwan ba>>Jama’ar Kebbi

Siyasa, Uncategorized
Ambaliyar Ruwa data afkawa Jihar Kebbi ta lalata Amfanin Gona da kuma gidaje da dama, wasu da lamarin ya shafa sun bayyana cewa rabonsu da ganin tashin hankali irin wannan tun shekaru da dama da suka yabata.   Shugaban karamar hukumar Kalgo, Muhammad Shamsudden Kalgo yayi bayanin cewa ko akalla gidaje 150 ne Ambaliyar ruwan ta lalata. Yace akwai kuma mutane 100 da suka tagayyara dalilin Ambaliyar ruwan, wasu sun koma zama tare da danginsu.   Yace amma sun godewa Allah babu wanda ya rasu sanadiyyar Ambaliyar ruwan saidai shekaru 100 baya babu wanda yaga irin wannan ambaliyar ruwa.   Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai taimakawa wanda ambakiyar ruwan ta shafa. Ya aikawa wakilai na musamman jihar ta Kebbi karkashin jagorancin Ministan No...
Sarkin Musulmi ya Bukaci da gwamnatin tarayya ta taimakwa wadanda Ambaliyar Ruwa ta shafa a jihar Kebbi

Sarkin Musulmi ya Bukaci da gwamnatin tarayya ta taimakwa wadanda Ambaliyar Ruwa ta shafa a jihar Kebbi

Kiwon Lafiya
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, a ranar Juma'a ya jajantawa Gwamnatin jihar Kebbi da jama'arta kan Annobar ambaliyar ruwa da ta auku a jihar. Sarkin Musulmin wanda ya kai ziyarar jajantawar ga Gwamna Atiku Bagudu a Birnin Kebbi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka wa dukkan jihohin da ambaliyar ta lalata, da kuma wadanda abin ya shafa. Abubakar ya kuma tausaya wa gwamnatin jihar da kuma mutanen jihar kan ambaliyar kwanan nan da ta lalata gonaki, gidaje tare da haifar da mutuwar mutane da dama a jihar. A jawabin Gwamnan ya godewa mai alfarma Sarkin Musulmi bisa wannan ziyarar tare da yi masa ta'aziyya game da rasuwar Hakimin Aliero, Alhaji Salihu Muhammad II, wanda ya mutu a ranar Juma'a.
Gwamnan jihar Kebbi ya sha Al’washin tai makawa Monoman da Ambaliyar Ruwa ta ci Gonakin su

Gwamnan jihar Kebbi ya sha Al’washin tai makawa Monoman da Ambaliyar Ruwa ta ci Gonakin su

Uncategorized
Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya jajantawa manoma da ambaliyar ruwa ta lalata gonakin su, tare da basu tabbacin cewa  gwamnati zata samar da ingantattun iri da sauran kayan aikin gona da ake bukata don ba su damar komawa gonakinsu da zarar ruwan ambaliyar ya janye. Gwamnan ya kuma yi alkawarin shiga tsakani wajen fadada rancen manoman. Gwamna Bagudu ya bayar da wannan tabbacin ne yayin ziyarar da ya kai wa wasu al'ummomin da ambaliyar ta shafa a kananan hukumomin Dandi da Koko Besse.   Da yake jawabi tun farko, Shugaban Kauyen Tungar Rahi, Alhaji Rabiu Hakimi, wanda ya yi magana a madadin manoman, ya roki gwamnan da ya shiga tsakani a madadinsu domin jinkirta biyan bashin manoma har zuwa 2021. Da yake amsawa, Gwamna Bagudu ya ba su tabbacin cewa zai shiga ...
Mutane 32 ne suka rasa rayukansu, gidaje da dama suka lalace sanadiyyar Ambaliyar ruwa a Jihar Kebbi

Mutane 32 ne suka rasa rayukansu, gidaje da dama suka lalace sanadiyyar Ambaliyar ruwa a Jihar Kebbi

Uncategorized
Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa akalla mutane 32 ne suka rasa rayukansu yayin da gidaje suka rushe wanda hakan ya tursasawa mutane da dama zama 'yan Gudun Hijira a jihar.   Hukumar kula da yanayi ta kasa, NiMET ta yi kintacen cewa kananan hukumomi 11 ne cikin 20 na jihar da ambaliyar ruwan zata taba amma zuwa yanzu Ambaliyar ta shiga kananan hukumomi 15, sauran 6 ma da suka rage na fuskantar barazanar Ambaliyar. Matsugunan 'yan Gudun Hijira 10 ne suka bayyana dalilin wannan matsala inda matsalar ta yaba gidan yari na Bagudu wanda dole saidai dauke mazauna gidan yarin aka yi zuwa gidan yarin Birnin Kebbi.   Gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu yayin ziyarar da ya kai wasu daga cikin garuruwan da lamarin ya faru ya bada umarnin a kaiwa al'umma tallafin kayan A...
Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin tallafawa wadanda ambaliyar ta shafa a Kebbi

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin tallafawa wadanda ambaliyar ta shafa a Kebbi

Kiwon Lafiya
Gwamnatin Tarayya a ranar Asabar ta yi alkawarin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Kebbi domin rage barnar da ambaliyar ta haifar a jihar.   Ministan Noma da Raya Karkara, Alhaji Sabo Nanono, shine ya yi wannan alkawarin a Argungu yayin wata ziyarar ban girma da suka kaiwa Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Mera, don jajantawa wadanda ambaliyar ta shafa a duk fadin jihar.   Nanono, wanda ya samu rakiyar Gwamna Atiku Bagudu da wasu jami’an Gwamnatin Tarayya da na Jiha, ya ce gwamnatin tarayya ta damu da mummunar ambaliyar da ta auku a jihar da sauran sassan kasar.   Ya ce ya je jihar ne domin ganewa Idon sa irin barnar da ambaliyar ta yi.   Hakanan Ministan ya bukaci manoma da kada su karaya, Inda  ya kara da cewa, ana ci gaba da kokarin samar musu da irin shinkaf...
Ambaliyar ruwa: Gwamna Bagudu ya ba da umarnin rarraba kayan agaji cikin gaggawa a jihar Kebbi

Ambaliyar ruwa: Gwamna Bagudu ya ba da umarnin rarraba kayan agaji cikin gaggawa a jihar Kebbi

Kiwon Lafiya
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya ba da umarnin raba abinci, ruwa da magunguna kai tsaye ga al'ummomin da ambaliyar ta lalata mazaunan su a Bagudu da Kende a cikin jihar. Bayan haka kuma, gwamnan ya bayar da umarnin gaggauta gina karin bandakuna ga mutanen da ambaliyar ta kora daga garuruwansu. Gwamna Bagudu, wanda ya yi tafiya mai nisa don ganin irin barnar da ambaliyar ta yi a yankunan, inda ya jajanta musu game da halin da suka tsinci kansu. Haka zalika Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta taimaka wa wadanda ambaliyar ta rutsa da su don sake gina gidajensu da su rushe sanadin iftila'in.
Yanzu-Yanzu: Jihar Kebbi ma na shirin yin fatali da gargadin gwamnati dan bude makarantu a 21 ga wannan watan

Yanzu-Yanzu: Jihar Kebbi ma na shirin yin fatali da gargadin gwamnati dan bude makarantu a 21 ga wannan watan

Siyasa
Gwamnatin jihar Kebbi na shirin bin sahun jihohin Legas, Kogi, da Osun wajan bide makarantun jiharta a wannan watan.   Gwamnatin jihar tuni ta fara rabon kayan kariya irinsu takunkumin rufe baki da hanci da kuma abin wanke hannu da sauransu zuwa makarantu 2008 dake fadin jihar. Kwamishinan Ilimi na matakin Farko da Firamare da Sakandare, Alhaji Muhammad Magawata Aleiro ne ya bayyana haka a wajan rabon kayayyakin. Yace suna bada shawarar a bude makarantun nan da ranar 21 ga watannan na Satumba amma shawarace a duba aga idan ta yi.   Ya kuma godewa gwamnan jihar, Atiku Bagudu bisa goyon bayan da yake baiwa bangaren Ilimi a jihar.