fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tag: Jihar Kogi

Ba za fa mu taba yadda ba, Har yanzu babu me Coronavirus/COVID-19 ko daya a Kogi, Tallar cutar kawai ake>>Inji Gwamnatin jihar Kogi

Ba za fa mu taba yadda ba, Har yanzu babu me Coronavirus/COVID-19 ko daya a Kogi, Tallar cutar kawai ake>>Inji Gwamnatin jihar Kogi

Siyasa
Gwamnatin jihar Kogi ta ci gaba da nacewa akan bakarta na cewa babu ko da mutum 1 dake da cutar Coronavirus/COVID-19 a jiharta.   Yace ba zata baiwa NCDC goyon baya a bayyana mutanen karya da cewa wai suna dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 ba duk da yawan masu cutar da ake samu a Najeriya.   Kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da Independent inda ya kuma musanta zargin NCDC na cewa Gwamna Yahaya Bello na musu zagon kasa a aikinsu.   Yace gwamna Yahaya Bello ba wai ya ki bada hadi  kai a samar da tsarin Lafiya bane amma yaki bada hadin kai ne a yi karya dashi. Yace ai a baya, NCDC ta yabawa jihar Kogi kan yakar zazzabin Lassa wanda nesa ba kusa ba ya fi cutar Coronavirus/COVID-19 da ake tallatawa. Yace kaw...
Yan Bindida sun kashe mutane 3 a yayin sallar Asuba a Kogi

Yan Bindida sun kashe mutane 3 a yayin sallar Asuba a Kogi

Siyasa
Wasu mahara da safiyar yau, Alhamis sun kaiwa kauyen Okofi dake jihar Kogi hari inda suka kashe masallata 3.   Shaidu sun bayyana cewa maharan sun kashe Limamin dakw jan sallar Asuba da kuma mamu 2 sannan mutane 2 sun jikkata. Kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN ya ruwaito kakakin 'yansandan jihar, William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kai jami'an tsaro kauyen.   Gunmen in the early hours of Thursday invaded Okofi community in Kogi, killing three persons and injuring two others.   Eyewitnesses told newsmen that the attackers invaded the community when the Muslim faithful were observing the early morning prayers in the community’s only mosque.   Confirming the incident, the state police command spokesman, DSP William A...
Tirsasawa ‘yan Najeriya aka yi suka yadda da Coronavirus/COVID-19>>Gwamna Yahaya Bello

Tirsasawa ‘yan Najeriya aka yi suka yadda da Coronavirus/COVID-19>>Gwamna Yahaya Bello

Siyasa
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ci gaba da rike matsayarsa ta cewa ana yayata cutar Coronavirus/COVID-19 ne kawai dan sakawa mutane fargaba da tsoro.   Ya kuma yi zargin cewa an kawo cutarne dan a rage yawan mutane inda yace da karfi da yaji aka sa 'yan Najeriya suka amince da wanzuwar cutar. Gwamna Bello ya bayyana hakane a wajan rasuwar alkalin alkalan jihar, Nasir Ajana inda yaje gaisuwa, ya bayyana cewa ba Coronavirus/COVID-19 ce ta kashe marigayin ba.   Ya kuma ce an kawo cutar ne kawai dan rage yawan mutane da sa su mutu da wuri inda yace babu abinda ya fi kisa da wuri kamar fargaba.
Gaskiya ban ji dadin komawar gwamnan Edo, Godwin Obaseki jam’iyyar PDP ba>>Gwamna Yahaya Bello

Gaskiya ban ji dadin komawar gwamnan Edo, Godwin Obaseki jam’iyyar PDP ba>>Gwamna Yahaya Bello

Siyasa
Gwamnan jihar Kogi,Yahaya Bello ya bayyana cewa kwata-kwata bai ji dadin komawar abokin aikinsa, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki jam'iyyar PDP ba.   Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai a fadar gwamnatin tarayya bayan ganawar da gwamnonin Arewa ta tsakiya suka yi da sakataren gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari a yau. Da yake amsa tambaya daga manema labarai kan cewa shin ko APC zata iya kwace kujerar gwamnan daga hannun Obaseki? Yahaya Bello yace a baya an ga yanda wanda bai da mulki a hannunshi ya kwacewa me mulki mulki, watau Shugaban kasa, Muhammadu Buhari daya kwace mulki a hannun Jonathan,  yace dan haka kwace gwamnan Edo daga hannun PDP abune me sauki.   Yace amma gaskiya komawar gwamna Godwin Obaseki jam'iyyar PDP kwata-kwata b...
Bamu yadda ba, bamu san inda kuka samoshi ba>>Jihar Kogi ta yi fatali da karin me Coronavirus/COVID-19 1 da NCDC tace an samu a jihar

Bamu yadda ba, bamu san inda kuka samoshi ba>>Jihar Kogi ta yi fatali da karin me Coronavirus/COVID-19 1 da NCDC tace an samu a jihar

Kiwon Lafiya
Hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC a bayanan da ta fitar yau, ta ce an samu karin mutim 1 me Coronavirus/COVID-19 a jihar Kogi wanda hakan ya kawo yawan masu cutar a jihar zuwa 3.   Saidai kamar yanda aka yi na farko, a ya zu ma jihar Kogi tace sam bata san da wannan zance ba. Kwamishinan lafiya na jihar ta Kogi,Dr. Haruna Saka ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar yau,Alhamis,Kamar yanda Hutudole ya samo. Yace sam basu yadda da karin mutum 1 me Coronavirus/COVID-19 da akace sun samu ba inda yace NCDC dai bayata dauki samfur din jinin kowa ba a Kogi to ta yaya ta samu karin mutum 1 a jihar?   Koda mutum 2 na farko da NCDC tace sun kamu da cutar a jihar, saida aka sha irin wannan dambarwa inda jihar ta Kogi tace bata yadda ba.
Ka fito ka baiwa mutanen Kogi hakuri>>PDP ta gayawa Gwamna Yahaya Bello

Ka fito ka baiwa mutanen Kogi hakuri>>PDP ta gayawa Gwamna Yahaya Bello

Kiwon Lafiya
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya kamata ya fito ya baiwa mutane hakuri saboda yanda yawa maganar cutar Coronavirus/COVID-19 rikon sakainar kashi.   Sakataren watsa labarai na jam'iyyar,  Kol Ologbondiyan ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace gwamna Bello bai nuna halayya irin ta shugaba ba a lokacin da ake tsaka da cutar. Yace gwamnan be rabawa mutanen jihar Kayan tallafi ba hakanan kwamitin da ya saka yayi yaki da cutar shima be bashi kudin aikin da ya kamata ya gudanar da aikin ba.   Gwamna Yahaya Bello dai ya bayyana cewa,ya saka dokar hana zirga-zirga a karamar hukumar Kabba onda aka samu mutum na farko da cutar ta kama.   Kola wanda shima daga karamar hukumar ya fito ya bayyana cewa, mutanen karamar huku...
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kogi ya saka dokar hana zirga-zirga a Karamar hukumar Kabba/Bunu inda me Coronavirus/COVID-19 na farko ya bayyan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kogi ya saka dokar hana zirga-zirga a Karamar hukumar Kabba/Bunu inda me Coronavirus/COVID-19 na farko ya bayyan

Kiwon Lafiya
Gwamnatin jihar Kogi ta saka dokar hana zirga-zirga a karamar hukumar Kabba/Bunu na tsawon kwanaki 14 bayan bayyanar mutum na farko da cutar Coronavirus/COVID-19 ta kama.   A baya dai an ruwaito cewa babban limamin Kabba, Ahmad Ejubunu da wani nanhannun damarsa sun kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 inda aka kaisu Asibiti a Lokoja daga nan kuma aka kaisu Abuja inda acan aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.   Da farko jihar ta karyata cewa babu wanda ya kamu da cutar a jihar inda tace bata yadda da sakamakon hukukar NCDC amma a yanzu ta saka dokar hana zirga-zirga a karamar hukumar.   Gwamnan a cikin sanarwar daya fitar ga jihar ya bayyana cewa likitocin da suka duba mutumin suma su killace kawunansu.
Coronavirus/COVID-19 a jihar Kogi gaskiyace, Nasan mutum 1 data kama>>Sanata Dino Melaye

Coronavirus/COVID-19 a jihar Kogi gaskiyace, Nasan mutum 1 data kama>>Sanata Dino Melaye

Siyasa
Tsohon sanatan Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, cutar Coronavirus/COVID-19 a jihar gaskiyace.   An dai samu rashin jituwa tsakanin NCDC da jihar Kogi inda NCDC tace jihar ta Kogi ta samu mutane 2 na farko da suka kamu da cutar amma jihar tace ba gaskiya bane. A sanarwar da ya fitar, Melaye ya bayyana cewa daya daga cikin mutanen da cutar ta kama a jihar yana garin Kabba ne kuma daga asibitin Lokoja aka aikashi zuwa Abuja.   Yace yasan mutumin kuma yana fatan wanda suka yi ma'amala dashi zasu mika kansu dan a musu gwaji. Yace ba zai zama cikin masu wasa da rayuwar jama'arsu ba.
Bamu yadda da NCDC ba yaudarar Najeriya kawai suke>>jihar Kogi

Bamu yadda da NCDC ba yaudarar Najeriya kawai suke>>jihar Kogi

Uncategorized
Jihar Kogi da a karin farko ta samu mutane 2 masu dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 wanda amma tace bata yadda da haka ba ta zargi hukumar NCDC da yaudarar 'yan Najeriya.   Kwamishinan watsa labarai na jihar,Kingsley Fanwo ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da gidan talabijin din Channelstv kamar yanda Hutudole ya samo. Fanwo yace NCDC na da aniyar sai ta ga cutar Coronavirus/COVID-19 ta shiga kowace jiha a kasarnan sannan kuma tana so a rufe Najeriya gana daya.   Yayi zargin cewa NCDC yaudarar 'yan Najeriya kawai take, jihar su bata da Coronavirus/COVID-19 amma sai da hukumar ta yi kutin-kutin aka sami cutar a jihar, gashi tattalin arziki ya shiga wani hali.   Ya kara da cewa ga cututtuka da yawa nan na kashe mutane, misali Malaria ta kashe muta...