
‘Yan sanda sun kama wasu mazauna Legas su 76 saboda’ keta ‘ka’idojin cutar coronavirus
A ranar Asabar din da ta gabata ne rundunar ‘yan sanda ta Jihar Legas ta cafke wasu mazauna Legas su 76 saboda keta ka'idojin cutar COVID-19 ta hanyar gudanar da bukukuwa.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, PPRO, Muyiwa Adejobi ya fitar ta ce an kama wadanda ake zargin ne da misalin karfe 1 na dare a wajen bikin ranar haihuwa wanda ya keta ka'idojin da hukumar ta sanya.
Wadanda aka kama a wurin bikin sun hada da: 1. Popoola Michael 2. Adeyemo Opeyemi 3. Ramon Salami 4. Kareem Akeem 5. Balogun Nurudeen da sauransu 71.