fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Jihar Nasarawa

Gwamanan Jihar Nasarawa ya yi Allah wadai da kisan Shugaban APC a jihar

Gwamanan Jihar Nasarawa ya yi Allah wadai da kisan Shugaban APC a jihar

Crime
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi Allah wadai da kisan shugaban jam'iyyar (APC) na jihar, Mista Philip Shekwo, inda ya bayyana kisan a matsayin abin takaici kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya  NAN ya rawaito. A safiyar Lahadi ne dai BBC ta samu labarin cewa ‘yan bindiga sun sace shugaban Jam’iyyar APC reshen jihar, Mista Philip Tatari Shekwo. A wata sanarwa da mai magana da yawun 'yan sandan jihar Nasarawa ya fitar Rahman Nansel ya tabbatar wa BBC da mutuwar Mista Philip Tatari Shekwo, wanda ‘yan bindiga suka sace a gidansa a daren Asabar. Rahotannin sun bayyana cewa, Yan bindigar sun kutsa gidan Mista Philip da misalin 11:00 na daren Asabar inda suka ɗauke shi, a cewar ‘yan sandan.  
Gwamnatin Jihar Nasarawa Zata Kashe Sama Da Biliyan 14 domin Ginin Katafariyar Sakatariyar Jihar

Gwamnatin Jihar Nasarawa Zata Kashe Sama Da Biliyan 14 domin Ginin Katafariyar Sakatariyar Jihar

Uncategorized
Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar Nasarawa Honorabul Dogo Shammah a ranar Litinin ya ce gwamnati jihar za ta gina katafariyar sakatariyar jihar da za ta lakume naira biliyan 14 a Lafia babban birnin jihar. Ya bayyana hakan ne ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Lafia. Ya ce sabon aikin yana cikin kunshin kasafin kudin da gwamnan jihar zai gabatar a ranar 17 ga wannan watan. A cewar sa manufar samar da sakatariyar shine maido da ofishoshin gwamnati guri guda.
Gwamnan Nasarawa ya gana da shugaba Buhari kan matsalar Tsaro

Gwamnan Nasarawa ya gana da shugaba Buhari kan matsalar Tsaro

Siyasa
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sulw ya gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari da yammacin yau, Talata akan matsalar tsaron data addabi jiharsa.   Bayan ganawar, Gwamnan ya bayyanawa manema labarai cewa jiharsa na fama da tashe-tashen hankula. Hutudole ya fahimci gwamnan yace masu yin wannan aika-aika wanda kwanannan suka kashe wani Basarake ba daga jihar suke ba. Ya tabbatar da cewa, wadannan mutane daga yankin Arewa maso gabas da kuma Arewa maso yammane suka fito. Hutudole ya ruwaito muku cewa Gwamna sule ya bayyana cewa tsaunuka dake jihar ne yasa 'yan bindigar suka je dan neman mafaka.   Yace amma mafarautansu da 'yan banga sun fi 'yan bindigar sanin garin. Gwamnan ya kara da cewa ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajan kokarin kare kansu. Hutudole ya tattar...
Bidiyo:Yanda Dakarun Najeriya suka kwato makamai a hannun ‘yan Ta’adda a Benue da Nasarawa

Bidiyo:Yanda Dakarun Najeriya suka kwato makamai a hannun ‘yan Ta’adda a Benue da Nasarawa

Tsaro
Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana yanda dakarun soji suka kwato bindigu da harsasai a hannun 'yan bindiga daga jihohin Nasarawa da Benue.   A Benue, Dakarun sun kai samamene kan maboyar dan ta'addarnan Gana da ake nemansa Ruwa a jallo, duk da cewa ya tsere da harbin bindiga a jikinsa, an kama wasu yaranshi da makamai. Hakanan a Nasarawa kuwa 'yan kabilar Bassane aka kama da makamai yayin da suke shirin kaiwa kabilar Tiv hari saboda rashin jituwa kan wasu filaye. https://twitter.com/DefenceInfoNG/status/1261989046995337216?s=19 Sojojin Najeriya dai sun dage da yaki da rashin tsaro a kasarnan tun daga kan Boko Haram zuwa 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane.
Hotuna: Matashi dan shekaru 30 ya kashe kansa a Jihar Nasarawa

Hotuna: Matashi dan shekaru 30 ya kashe kansa a Jihar Nasarawa

Uncategorized
Wani matashi da aka fisani da  suna james Samuel mai kimanin shakara 30 a duniya ya rataye kansa a wani aji  a cikin wata makarantar gwamnati ta gaba da pramary da ke Gurku ta karamar hukumar Karu a jahar Nasarawa. An samu gawar mutumin a ranar juma'a A rataye An samu  labarin aukuwar haka ne a wurin wani  mauzaunin yankin wanda kuma ya kasance dan sanda ne mai aiki a Abuja,inda yayi gaggawar kai rahoton aukuwar lamarin a ofishin yan sanda mafi kusa. An samu hoton mamaci da na wata mata wanda aka bayyana ta a matsayin mahaifiya ga mamamacin,Bayan zuwan yasanda ne aka sauko da gawan mamacin daga inda take. Shugaban Kabilar Tiv ta garin Gurku,wanda aka fisani da Samuel, mahaifi ga mamacin ya bayyana a wurin da abun ya faru shi da sauran ya'yan shi inda yayi kuka har y...
Jihar Nasarawa ta saka dokar hana zirga-zirga a garin dan majalisar da Coronavirus/COVID-19 ta kashe

Jihar Nasarawa ta saka dokar hana zirga-zirga a garin dan majalisar da Coronavirus/COVID-19 ta kashe

Uncategorized
Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana saka dokar hana zirga-zirga a karamar hukumar Nasarawa inda daga nanne dan majalisar jihar da cutar Coronavirus/COVID-19 ta kashe ya fito.   Kwamishinan yada labarai da Al'adu na jihar, Dogo Shamma ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan ganawar da gwamnatin tayi dan duba yanda lamuran cutar suke a jihar.   A baya dai gwamnan jihar, Abdullahi Sule ya tabbatar da cewa cutar Coronavirus/COVID-19 ce ta kashe dan majalisar, Sulaiman Adamu.   Akwai mutane 74 da a yanzu haka jihar ke nema wanda suka yi ma'amala da dan majalisar. Jihar ta kuma saka dokar amfani da abin rufe fuska na dole.   Sannan Kwamishinan Shari'a na jihar, Dr. Abdulkarim Abubakar Kana ya bayyana cewa an sassauta dokar hana zirga-zirga ta Ka...
Ya rasa ransa lokacin da ya ke bugawa kulaf dinsa kwallo

Ya rasa ransa lokacin da ya ke bugawa kulaf dinsa kwallo

Wasanni
Wani abun tausayi ya faru a daya daga cikin wasannin Kwallon Kafa na Najeriya a ranar Lahadi yayin da dan wasan Nasarawa United, Chieme Martins, ya fadi kasa ya rasa ransa.   A cewar shaidu, Martins ya fadi cikin rauni ne bayan wata arangama da ya yi da wani dan wasan Katsina United a ranar Lahadin da ta gabata, a kokarin ceto ransa ne bayan an garzaya dashi asbiti yace ga garin ku nan.   A lokacin, dan wasan ya fadi kasa warwas sannan daga baya aka garzaya da shi Asibitin kwararru na Dalhatu-Araf da ke Lafia inda Likitoci suka ce ya mutu.
Gwamnatin Jihar Nasarawa Za Ta Mayar Da Almajirai Dubu 63,000 Zuwa Jihohinsu Na Asali

Gwamnatin Jihar Nasarawa Za Ta Mayar Da Almajirai Dubu 63,000 Zuwa Jihohinsu Na Asali

Uncategorized
Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana kudirinta na dawo da dukkanin yara Almajirai da ke kasa da shekara 10, zuwa ainahin jihohinsu, kamar yadda Daily Nigeria ta ruwaito.   Kwamishina mai kula da harkokin mata ta jihar, Halima Jabiru ce ta ba da sanarwar yayin wani taron manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar a Lafia, babban birnin jihar.   Misis Halima ta lura cewa jihar tana da Almajirai kimanin dubu 63 wadanda suke yawo kan tituna.   A cewarta, sake haduwa da wadannan yaran zuwa ga iyayensu zai yi wa duniya kyau da al'umma baki daya.   Ku tuna cewa gwamna Abdullahi Sule ya ba da umarnin zartarwa wanda ya ayyana daurin shekaru 10 a gidan yari ga iyayen yaran da yaransu suke yin bara kan tituna a cikin jihar.   G...