fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Jihar Osun

Hukumar sojin sama ta sanar da kama sojojin da suka ci zarafin mutane a Osun

Hukumar sojin sama ta sanar da kama sojojin da suka ci zarafin mutane a Osun

Tsaro
Hukumar sojin sama ta sanar da kama jami'anta da aka gani a wani bidiyobda ya watsu sosai a shafukan sada zumunta suna cin zarafin wasu matasa.   An bayyana cewa lamarin ya farune a Ilesha, Jihar Osun. Sanarwar hukumar sojin ta bayyana cewa, ana kan binciken sojojin kuma idan an kammala za'a dauki matakin da ya dace akansu.   Hukumar tace wannan abin da aka ga sojojij sun yi ba abinda aka koya musu kenan ba, saboda duk wani da ake zargi to ana kallonshi a matsayin wanda bashi da laifi har dai idan kotu ta tabbatar masa da laifin.
Wanda suka saci kaya a jihar Osun sun fara mayar dasu ga gwamnati

Wanda suka saci kaya a jihar Osun sun fara mayar dasu ga gwamnati

Siyasa
Rahotanni daga jihar Osun na cewa wanda suka saci kaya daga shagunan 'yan kasuwa masu zaman kasu da kuma rumbunan Ajiya na Gwamnati tuni sun fara mayar da kayan bayan gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola yace ya basu awanni 72 na Afuwa su mayar da kayan da suka wawusa.   Gwamnan a lokacin da ya je ziyarar Gani da ido ya sanar da cewa ya baiwa mutanen Jihar Afuwar awanni 72 su dawo da kayan da suka sata ko kuma a bisu har gida a kwato. Da dama sai sun amsa wannan kira na gwamnan, shugaban dake kula da mayar da kayan, wanda kuma mataimakin shugaban ma'aikatan gwamnan jihar ne, Abdullah Binuyo ya tabbatar da cewa mutane na bada hadin kai kuma suna jin dadin hakan.   Saidai yace akwai sauran kayayyakin da aka sace din da yawa, wanda har yanzu suna hannun mutane. Yace ...
Fashewar tankar dakon mai ya lakume rayukan mutane 12 a Osun

Fashewar tankar dakon mai ya lakume rayukan mutane 12 a Osun

Uncategorized
Akalla mutane 12 ne rahotanni suka bayyana cewa sun kone kurmus sanadiyyar fashewar tankar dakon mai wanda ya faru a kan babbar hanyar Ilesa-Akure, A jihar Osun, ranar Litinin. Hatsarin wanda ya afku a Erin-Ijesha, wani gari da ke karamar hukumar Oriade ta jihar, ya jefa mazauna yankin cikin wani yanayi na jimami. Rahotanni sun bayyana cewa, motar dakon mai din, bayan ta fadi ta kwaranyar da abin da ke cikinta a kasa, wanda hakan ya haifar da conkoson ababan hawa a kan babbar hanyar.   Jaridar Tribune ta rawaito cewa fashewar tankar wanda ya faru da rana ya kara cunkoson ababen hawa kafin isowar jami'an kashe gobara da jami'an hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) wadanda daga karshe suka shawo kan al'amura. Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa ya dauki ma’aikatan k...
Dan Kasuwan Ya Kashe Kanshi A Jihar Osun

Dan Kasuwan Ya Kashe Kanshi A Jihar Osun

Uncategorized
Wani dan kasuwa, Festus Olawale, ya kashe kansa a cikin shagon sayar da cocoa da ke Gbongan, jihar Osun. Marigayin, dan kasuwa ne da ke harkar cocoa, ya mutu bayan ya rataye kansa a daya daga cikin dakuna a cikin shagon sayar da kayan cocoa da ke Oke Ola, Gbongan ranar Juma’a. Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 8:00 na dare, ya haifar da fargaba a yankin lokacin da aka gano gawar tana rataye a cikin dakin.  Mahaifan yara hudu, an kuma gano, bai bar bayanin kashe kansa ba kuma bai yi wani abin mamaki ba kafin abin ya faru. Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kuma ce kawo yanzu ba a san dalilin kisan ba. Mai magana da yawun rundunar, Yemisi Opalola, a ranar Lahadi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami'an 'yan sanda sun ziyarci wurin. Ya ce, “Daga ...