
Wasu Fusatattun Matasa A jihar Oyo su bankawa wata motar Daukar Shanu wuta
Rahotanni daga Jihar Oyo na nuni da cewa, wasu fusatattun Matasa dake a yankin Saki sun kone wata Motar Dakwan shanu wadda ke Dauke da shanu 25 sakamakon buge wani yaro da Direban motor yayi.
A cewar wani Mazaunin yankin mai suna Adekunle Lawal wanda ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne Da misalin karfe 10 na dare inda wani Diraban motar Dakwan shanu ya buge wani yaro dake tuka babur wanda ta kai ga har ya rasa ransa.
A cewarsa kafin A tuntubi Jami'an tsaro ne wasu fusatatun Matasa suka bankwa motar wuta wadda ta kai ga konewa kurumus kamar yadda ya shaida hakan ga Jaridar Sun.
Shima Jami'in hulda da Jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Olugbenga Fadeyi, ya shaida yadda lamarin ya faru inda kuma ya tabbatar da mutuwar yaron da motor ta buge.