
Rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba ta yi Nasarar cafke wasu masu garkuwa da Mutane
Rundunar 'yan sandan jihar Taraba tayi Nasarar kama mutane tara da ake zargi da yin garkuwa da wani Dan Majalisar Dokokin jihar Mohammed Bashir Bape, wanda aka sace shi tun a watan Disamban shekarar 2020.
An kama wadanda ake zargin ne a maboyarsu dake a Jihohin Taraba da Filato bayan wani bincike da rundunar ‘yan sanda ta gudanar domin cafke masu laifin.
Wadanda ake zargin sun hada da, Yusuf Abubakar, mai shekaru 31 dan asalin karamar hukumar Jalingo dake a jihar Taraba, sai Muntari Umar, mai shekaru 27, dan asalin karamar hukumar Mayo Belwa ta jihar Adamawa, Ahmadu Dahiru, mai shekaru 28, dan asalin karamar hukumar Lau, jihar Taraba, Ali Alhaji Wurungo mai Shekaru 25, dan asalin karamar hukumar Lau ta jihar Taraba, Buhari Nuhu, dan shekaru 25, dan asalin karamar hukumar Jalingo, Moh...