fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Jirgin Kasa

Kuma Dai:Kalli Bidiyon yanda jirgin kasa dake Jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna ya sake tsayawa a tsakiyar daci karfe 2 na dare

Kuma Dai:Kalli Bidiyon yanda jirgin kasa dake Jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna ya sake tsayawa a tsakiyar daci karfe 2 na dare

Tsaro
Ba'a dade ba aka samu Rahoton cewa jirgin kasan dake Jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna ya samu tangarda inda har hakan yasa Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya bada hakuri kan lamarin.   To saidai a karo na 2, Jirgin ya sake tsayawa a tsakiyar Daji kuma wajan karfe 2 na Dare. TheNation ta bayyana cewa jirgin ya tsaya har na tsawon kusan awanni 2 kamain daga baya ya ci gaba da aiki.   Amma an gani a Bidiyon Fasinjoji suna ta magana cikin bacin rai. Da aka tuntubi me kula da tashar jirgin kasar dake Rigasa. Aminu Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace matsalace irin wadda kowane inji bature ke samu aka samu kuma tuni aka gyara, jirgin ya ci gaba da aiki. https://www.youtube.com/watch?v=Wg1wfnPryIE Passengers stranded in bush as Kaduna/Abuja train breaks d...
Shugaba Buhari Ya Sanya Sunayen Tashoshin Jiragan Kasa Ga Tinibu, Osinbanjo Da Soyinka

Shugaba Buhari Ya Sanya Sunayen Tashoshin Jiragan Kasa Ga Tinibu, Osinbanjo Da Soyinka

Siyasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya sunayen tashoshin jirgin kasa a layin Legas zuwa Ibadan da Itakpe zuwa Ajaokuta zuwa Warri ga yan Najeriya da suka cancanta, in ji Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi. Daya daga cikin masu taimakawa shugaban kasa, Tolu Ogunlesi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wani twitter. A cewar Ogunlesi, an sanya sunan tashar ta Apapa ne ga Bola Ahmed Tinubu, yayin da aka Sanya wa tashar Agege ga Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola. Sauran mutanen da aka sanya sunayen su ga tashar jirgin sun hada da Lateef Jakande (tashar Agbado), Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo (tashar Kajola), da Funmilayo Ransome-Kuti (tashar Papalanto). Marigayi Mobolaji Johnson (tashar Ebute Metta), Wole Soyinka (tashar Abeokuta) Segun Osoba (tashar Olodo)...
An fara aikin Shimfida Titin Jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano

An fara aikin Shimfida Titin Jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an fara aikin shimfida titin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano.   Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya tabbatar da hakan inda yace yanzu haka an fara aikin daga bangaren jihar Kaduna. Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya tabbatar da fara aikin inda shima ya saka hotunan yanda aikin ya fara daga jihar Kaduna. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1285934515442135042?s=19 Aikin na daga cikin kokarin gwamnti na shimfida titin jirgin kasa daga Legas zuwa Kano.
Kasar Japan ta samar da Jirgin kasa mafi sauri wanda tace Zai iya Zillewa aukuwar girgizar kasa

Kasar Japan ta samar da Jirgin kasa mafi sauri wanda tace Zai iya Zillewa aukuwar girgizar kasa

Uncategorized
Kasar Japan ta samar da Jirgin kasa me saurin tafiyar 360kph da take idannaka samu girgizar kasa zai iya tsira da Fasinjojin cikinsa.   Ta sakawa Jirgin kasan Suna 700s. Tace yana amfani da wutar lanteki daga tashar jirgin kasar amma ta samar masa da wasu Batira wanda idan aka samu matsala zai koma aiki dasu. Tace akwai wata na'ura da aka saka dake gano motsin kasa, kuma muddin aka samu girgizar kasar, nan da nan jirgin zai katse amfani da wutar tashar jirgin ya koma amfani data batiran sannan ya tsaya a guri daya cak.   Kuma zai kai fasinjoji sa zuwa wani gurin da ba matsala a wannan yanayi. Kasar Japan ce dai kasar data fara samar da jirgin kasa mafi sauri a Duniya.
Daga Ranar Litinin me zuwa za’a daina jigilar fasinja a jirgin kasan Najeriya

Daga Ranar Litinin me zuwa za’a daina jigilar fasinja a jirgin kasan Najeriya

Uncategorized
Hukumar kula da safarar jirgin kasa ta Najeriya, NRC ta bayyana aniyar dakatar da ayyukan jigilar Fasinjoji a jirgin saman na Najeriya gaba daya daga nan zuwa Ranar Litinin.   Hakan na zuwane jim kadan bayan da aka gano karin mutane 10 dake dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 a Babban birnin tarayya,Abuja da kuma Legas.   Ranar 23 ga watan Maris kenan za'a daina jigilar fasinja ta Jirgin kasa a Najeriya.   A wani labarin me kama da wanna mun kawo muku cewa Gwamnatin tarayya ta rufe gaba dayan filayen jiragen sama