
Hotuna: Jirgin ruwa mafi girma ya zo gabar ruwan Najeriya
Jirgin ruwa mafi girma da ya taba zuwa Najeriya ya isa gabar ruwa ta Onne Port a garin Fatakwal jihar Rivers.
Jorgin tuwan me suna Maerskline Stardelhorn ya fitone daga kasar Singapore inda ya iso gabar ruwa ta Najeriya a jiya, Asabar. Hutudole ya samo muku cewa jirgin ruwan na da tsawon mita 300 da kuma fadin mita 48.
An aika jirgin ruwan zuwa Fatakwal ne dan a ragewa tashar jirgin ruwa ta Legas cunkoso.