fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Jirgin Sama

Shugaba Buhari ya saka daya daga cikin jiragen samansa a Kasuwa

Shugaba Buhari ya saka daya daga cikin jiragen samansa a Kasuwa

Siyasa
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya saka daya daga cikin jiragen samansa me suna, Hawker 400 a kasuwa.   A shekarar 2011 ne fadar shugaban kasa ta fara amfani da jirgin saman me daukar fasinjoji 9 da ma'aikata 3. Binciken Punch ya nuna cewa ana sayar da jirgin akam Dala Miliyan 22.91 a shekarar 2012. Gwamnatin tarayya ta tallata sayar da jirgin a jaridun Najeriya inda tace za'a iya dubashi a inda sauran jiragen shugaban kasar suke, ga me bukata.   A shekarar 2016, fadar shugaban kasar ta saka 2 daga cikin jiragen saman shugaban kasar a Kasuwa, Hakanan fadar ta yi alkawarin baiwa rundunar sojojin saman Najeriya wasu daga cikin jiragen saman shugaban kasar dan rage kashe kudi.
Tun Shekaru 3 da suka gabata hukumomin Najeriya suka hana amfani da jirgin saman da yayi hadari a Legas jiya saboda ya lalace

Tun Shekaru 3 da suka gabata hukumomin Najeriya suka hana amfani da jirgin saman da yayi hadari a Legas jiya saboda ya lalace

Uncategorized
Rahotanni sun bayyana cewa jirgi me saukar Angulu da yayi hadari jiya a Legas inda ya kashe mutane 3, tun shekarar 2017 hukumomin Najeriya suka hana shi ya ci gaba da tashi sama saboda abubuwa da yawa a cikinsa sun lalace.   A jiyane dai jirgin ya fadi a yankin Opebi dake birnin Legas inda nan take mutane 2 dake cikin jigin suka mutu sannan daga baya dayan da aka kai Asibitin shima Ya Mutu . Hutudole ya tattaro muku daga Rahoton Sahara Reporters cewa wata majiya tace an hana jirgin tashi. Majiyar ta kara da cewa kamfanonin sufurin jirage da dama sun yi amfani da wanan jirgi a baya inda suka rika neman a basu Lasisin aikin jirgin.
Ayyukan Jiragen Saman Cikin Gida Sun Koma Aiki Gadan-gadan a Filayen Jiragen Sama 14>>Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika

Ayyukan Jiragen Saman Cikin Gida Sun Koma Aiki Gadan-gadan a Filayen Jiragen Sama 14>>Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika

Siyasa
Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, a ranar Lahadin din nan ya sanar da cewa filayen jiragen sama 14 a duk fadin kasar nan sun koma cikakken aikin sufurin cikin gida. Sirika, wanda ya yi wannan sanarwar a shafin shi na Twitter @hadisirika. Ya kara da cewa wannan ya hada da ayyukan jirage masu zaman kansu da na shata, ya ce za a sanar da jama'a game da sauran filayen jirgin saman a lokacin da ya dace. Filayen jiragen saman goma sha hudu da aka amince su fara aiki da sufurin jirgin sama sune: Filin jirgin saman Murtala Muhammed, Legas; Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Abuja; Filin jirgin saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano, Kano; Filin jirgin sama na Fatakwal, Omagwa; Filin jirgin saman Sam Mbakwe, Owerri; Filin jirgin saman Maiduguri, Maiduguri; Filin jirgi...
Bayan kwana 102 jirgin farko ya tashi zuwa Abuja

Bayan kwana 102 jirgin farko ya tashi zuwa Abuja

Uncategorized
Jirgin fasinja na farko ya taso daga Legas zuwa Abuja, bayan kwana 102 da rufe zirga-zirgar jiragen sama saboda bullar cutar coronavirus a Najeriya.   Jirin farkon ya bar filin jirgin sama na Legs ne da misalin karfe 7.15 na safiyar Laraba, ranar da Gwamnatin Tarayya ta bude harkokin sufurin jirage na cikin gida. Rahotanni sun ce harkokin sufurin jiragen sama sun fara kankama a tashoshin inda ake sa ran jirgi na biyu zai tashi da misalin 11.00 na safe. Hukumar Sufuruin Jiragen Sama ta Kasa (NCAA) ta amince da sake bude bangaren cikin kiyaye dokokin kariyar cutar COVID-19.   An fara da tashoshin Legas da Abuja ne a ranar Laraba 8 ga wata Yuli inda ake sa ran jirage uku za su tashi tsakanin Legas da Abuja daga cikin jiragen kamfanoni shida da NCAA ta ba wa izini...
Da Dumi-Dumi:Gwamnati ta bayyana ranar dawo da zirga-zirgar jiragen sama

Da Dumi-Dumi:Gwamnati ta bayyana ranar dawo da zirga-zirgar jiragen sama

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar dawo da zirga-zirgar jiragen sama wanda aka kulle dalilin zuwan cutar Coronavirus/COVID-19.   Ministan Sufurin jiragen Sama, Hadi Sirika ne ya bayyana haka a yau, Laraba.   Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari,  Tolu Ogunlesi ya bayyana cewa Ministan ya sanar da dawo da zirga-zirgar jiragen sama kamar haka: Abuja da Legas, Ranar 8 ga watan Yuli.   Kano, Port Harcourt, Owerri, Maiduguri,  11 ga watan Yuli.   Sai kuka saura zasu dawo 15 ga watan Yuli.   Saidai yace babu ranar dawowar Sufurin jiragen kasa da kasa.
Dole fasinjoji su isa tashar jirgin sama a cikin awanni uku kafin a tashi>>Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa

Dole fasinjoji su isa tashar jirgin sama a cikin awanni uku kafin a tashi>>Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa

Kasuwanci
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) ta ce dole ne fasinjoji su isa awanni uku kafin lokacin tashin su alokacin da ayyukun tashin jirage ya fara aiki a filayen saukar jiragen saman a karshen wannan watan. Hukumar ta sanar da hakan ne a ranar Litinin a zaman wani sabon tsari don sake bayarda umarnin tashin jirage duk da ana  cikin wannan masifar cutar korona. Sanarwa data fito ta hanyar Twitter, ta ce zuwan matafiya da wurwuri zai ba da damar ingantaccen bincike da kuma dubawa kafin shigan su jirgi. Hukumar ta Kara da cewa, kuma an bukaci matafiya da su nisanci  juna na mita biyu a tsakanin su a filayen jirgin saman, yayin da da kara cewa ba za a kyale mutanen da ba sanya takun kumin fuska ba a cikin filayen jirgin saman. Shugaban kasa ya rufe filaye...
Najeriya ta kama wani jirgin sama daga Birtaniya saboda yin jigila

Najeriya ta kama wani jirgin sama daga Birtaniya saboda yin jigila

Uncategorized
Gwamnatin Najeriya ta kama wani jirgi na kamfanin Flair Aviation na kasar Birtaniya bayan zargin jirgin da laifin jigilar 'yan Najeriya zuwa kasashen ƙetare da kuma shiga da su ƙasar. Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya tabbatar wa BBC da kama jirgin a wata tattaunawa inda ya ce yanzu haka ana gudanar da bincike kuma jirgin zai biya tara mai matukar yawa. Ministan ya tabbatar da cewa jirgin yana jigilar mutane cikin Najeriya har zuwa jihohi kamar Abuja da Legas da kuma Oyo duk da annobar korona da ake ciki. Ya bayyana cewa an bai wa jirgin dama gudanar da ayyukan jin ƙai, amma ya ɓige da jigilar fasinjoji.