
Kungiyar ma’aikatan Lafiya ta JOHESU ta janye yajin aikin da ta ke
Kungiyar ma'aikatan Lafiya ta JOHESU ta janye yajin aikin da take inda ta bukaci membobinta da su koma bakin aiki daga yau, Litinin.
A sanarwar data fitar ta bakin shugabanta, Biobelemoye Josiah ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta yi burus da bukatun data gabatar mata dasu.
Tace maimakon ma gwamnatin ta biya mata bukatunta sai aka koma yi mata barazana da bata suna.
JOHESU tace dan hakane yasa a yanzu ta janye yajin aikin kuma zata fito da wasu sabbin dabarun da zata bi dan neman hakkinta.