
Jakadan Najeriya a kasar Jordan, Alhaji Haruna Ungogo, ya rasu yana da shekaru 70
Jakadan Najeriya a Jordan, Alhaji Haruna Ungogo, ya mutu yana da shekara 70.
Jami'in diflomasiyyar, wanda ya kasance tsohon sakatare a gwamnatin Kano da kuma tsohon Rector, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, ya mutu a asibitin Gwamnati da ke Garki, Abuja, ranar Lahadi bayan gajeriyar rashin lafiya.
A cewar majiyoyin daga iyalen shi, tuni shirye-shirye sun kankama don kai gawarsa Kano don yi masa jana’iza a yammacin ranar Lahadi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.